Sarki Sanusi: Najeriya Mai Abun Mamaki, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Assalamu Alaikum

To jama’ah, kamar dai yadda duk kuke biye da abubuwan da suke faruwa akan diramar da ke gudana a Masarautar Kano mai daraja, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje dai ya aika wa da Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II takardar tuhuma, wadda yaran sa da ya bai wa kwangila, kuma yake fada masu duk abunda za su yi, karkashin wani wai shi Muhyi Magaji, kuma yace yana so a amsa wannan tuhuma cikin wani dan lokaci! Wanda daga karshe, duk mun san manufar wannan azzalumin mutum, wanda ya ki bin umurnin kotu, ya nuna kotu bata isa ba, ya wulakanta tare da tozarta Masarauta; manufarsa shine yayi amfani da wannan rubabben rahoton, yace zai cire Mai Martaba daga kujerar sa!!!

Ya ku jama’ah! Idan kun lura sosai da wannan badakalar da ke faruwa a Kano, zaku fahimci cewa, ‘yan siyasar mu, tun daga Sama har kasa, wallahi ba al’ummah ne a gaban su ba, ba arewa ce a gabansu ba, kawai bin son zuciyar su ne a gaban su. Idan ba haka ba, ta yaya don Allah, mutumin da duniya ta shaida shi yana karbar cin hanci na miliyoyin daloli, duniya ta shaida shi barawo ne, wai zaya ce zai tuhumi mutumin da duniya ta shaida gaskiyar sa da amanar sa da kaunar ci gaban da yake dashi ga al’ummar sa?

Wace irin kasa ce wannan muke rayuwa a cikin ta? Yanzu haka arewar mu ta koma? Ya zamanto ana kallon mutum yana barna, amma kowa yayi shiru ya kasa cewa komai? Ina Shugaban kasa Muhammadu Buhari? Don Allah idan Gwamnan Katsina ne yake yiwa Sarkin Katsina haka za kayi shiru? Ina manyan mu na arewa? Yanzu haka za kuyi shiru, kuna kallo ana cin mutuncin Masarautar Kano, kun ki kuce komai? Kun ki ku dauki mataki? Don Allah bari in tambaye ku, idan da ace wannan abun da yake faruwa a Kano, a kudu ne yake faruwa, kuna ganin manyan su ba zasu dauki mataki ba? Kuna ganin za suyi shiru suna kallon wani Gwamna yana kama-karya? Haka fa kuka yi a al’amarin Boko Haram, kuka ki daukar kwakkwaran matakin da ya dace, sai da ya yiwa arewa babbar illa tukuna kuka farga! Yanzu ga sha’anin satar mutane domin karbar kudin fansa! Haba manyan arewa! Yanzu arewa bata da gata? Yanzu kenan ya zama ba masu fada aji a arewa? Yanzu Masarautun mu basu da gata kenan? Ko wane kucakin dan siyasa zai iya cin mutuncin su? Yanzu da ace Allah ya dawo da ran Mujaddidi Shehu Usman Dan Fodio, kuna ganin bakin ciki ba zai kashe shi ba akan wannan sakaci naku?

Yanzu Gwamna Gandujen da ya shahara da karbar cin hanci da rashawa, shine har yake da bakin ya tuhumi bawan Allah, salihi, irin Mai Martaba, Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II, mai daraja, wanda da ya sadaukar da kujerar sa ta Gwamnan Babban Bankin Najeriya don kwatar mutuncin arewa da yancin ‘yan arewa? Yanzu ku ‘yan arewa har kun manta da duk wannan, da har za ku bari mutumin da ko jahili ya shaida shi barawo ne zai wargaza maku tsari da lissafi? Ina EFCC? Ina ICPC? Ina ‘yan sandan Najeriya? Ina fadan da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari take cewa tana yi da cin hanci da rashawa?

Wallahi idan dai har wannan barawon kuri’un zaben da rana tsaka, yana da masaniya da ilimi na tarihi, ya kamata ya tuna da, ko kuma ya koyi darasi daga Shugaba Goodluck Jonathan, wanda shima ya taba yakar Sarki Sanusi a baya, kawai ba don komai ba sai don Sanusi ya fadi gaskiya. A lokacin, Shugaba Jonathan yayi amfani da karfin sa, ya taka doka, ya cire Sanusi daga zama Gwamnan Babban Bankin Najeriya. Amma abun tambayar shine, ina Shugaba Jonathan yake a yau? Ina yake? Meye matsayin sa? Shin har yanzu shine shugaban kasar Najeriya? Don haka wallahi, yadda Shugaba Jonathan ya bar kujerar mulki, haka nan sai Ganduje ya bar kujerar mulki! Sai ya zama bai da ta cewa a Kano. Kuma na rantse da Allah wanda babu abun bautawa da gaskiya sai shi, wallahi, sai Ganduje yayi dana-sanin duk wannan abun da yake yi a yanzu!

Kuma Alhamdulillahi, ko da Ganduje ya cire Sarkin Kano Sanusi a yau, tarihi ba zai taba yiwuwa ba a Masarautar Kano, dole sai an ambaci Sarki Sanusi.

Sannan dama shi Sarkin ya fada, ko an cire shi ko ba’a cire shi ba, wata rana za’a fita da gawarsa daga cikin gidan sarauta! Domin Sarki nawa akayi kafin sa? A yau ina suke? Saboda haka, Gwamna Ganduje yayi hankali, wallahi yabi duniya a sannu. Idan kuwa yaki ji, to ya sani, ba yaki gani ba!

Wassalamu Alaikum,

Dan uwan ku,

Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta daga Okene, Jahar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma +2348038289761.

Share.

game da Author