Sarakunan Ganduje Ba Sarakuna Bane, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

‘Yan uwa na masu daraja, ya kamata ku sani, wallahi sai mun yi yunkurin kare addinin mu da mutuncin mu da al’adun mu wadanda basu sabawa Musulunci ba sannan Allah zai taimake mu kuma makwabtan mu da abokan zaman mu su girmama mu kuma su mutunta mu. Amma wallahi matukar muka yi shiru, muka zuba ido wasu kucakan ‘yan siyasa suna yi muna wasa da addini, mutunci da al’ada, to sai an wayi gari mun zama banzaye, shashashu, wawaye. Kuma sai ya zamanto abokan zaman mu su rinka yi muna dariya, suna cewa, ai gashi nan ku ‘yan siyasar ku basu mutunta hurumin addinin ku da al’adunku; a duk lokacin da suka ga dama sai su wulakanta jagoran addinin ku da Sarkin ku! To irin wannan ne muke ta kokarin karewa ko da zamu rasa rayuwar mu, domin wallahi, addinin mu shine gatan mu, ko munki ko mun so; kuma ko mun yarda ko bamu yarda ba. Kuma Sarakunan nan namu da wasu wawayen ‘yan siyasa, kucakai, suke kokarin raina wa, wallahi ba wani munafukin da zai ce bai amfana dasu ba, ko bai karu da su ba. Sai dai in mutum butule ne kawai!

Wasu wawayen ‘yan siyasa, jahilai, kazamai, ‘yan maula, ‘yan kore, banbadawa, sun kira ni daga garin Kano, wai su magoya bayan Ganduje, suka zazzage ni, suka ci mutunci na, wai sai sun dauki mataki a kai na; har suke cewa wai kudi Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na II yake bani, shiyasa nike ta kokarin kare shi a koda yaushe! Shine nayi dariya, nike cewa, wadannan wallahi basu san da wanda suke magana ba. Ni zasu ce Sarki ya saye da kudi? To ai Sarkin yana nan raye, sai yayi masu bayanin nawa ya saye ni? Wadannan mutane sun makara wallahi. Domin mu babu kage da sharrin da ba’a yi ba a kan mu, don a dauke muna hankali, amma ba’aci nasara ba, balle wadannan kananan alhaki.

Imam Murtada Gusau

Imam Murtada Gusau

Idan maganar kudi ce, a lokacin Gwamnatin Jonathan, na rantse da Allah, wanda ba abun bautawa da gaskiya sai shi kadai, wasu ‘yan siyasa, kuma yanzu haka suna nan a raye, kuma nasan zasu karanta wannan rubutun nawa, idan har karya nike yi masu, to su karyata ni, ni kuma zan yi wani sabon rubutun in ambaci sunayen su karara, in yaso su kai ni kotu!

Wadannan ‘yan siyasa, Allah shine shaida na, sun same ni, suka ce suna roko na da in daina yin hudubobin Juma’ah da rubuce-rubucen da nike yi akan Shugaba Jonathan, zasu bani Naira miliyan goma.

Kuma za’a bani sabuwar mota da gida. Kuma duk shekara zan tafi Hajji da Umarah. A lokacin nace da su, ni ba domin neman kudi ko wani abun duniya nike yin rubutu na ba. Kuma maganar Hajji da Umarah, nace da su, wannan kiran Allah ne; a duk lokacin da Allah ya kira ni zan tafi. Nace da su, nayi shekara ashirin da biyar ina limamin Juma’ah, kuma ba karamin Masallaci ba, kuma masallaci ne sananne, amma wallahi, tun da nike ban taba yin aikin Hajji ba, kuma wallahi ban taba rokon kowa kujerar Makkah ba, idan kuma na taba rokon wani kujerar Makkah anan kasar, to kar ya rufa mani asiri, ya tona. Amma Umarah na tafi sau hudu a rayuwa ta, kuma wallahi ban taba roko a bani kujerar Umarah ba, Allah ne cikin ikon sa, zai bani, ina zaune za’a kira ni, ace in shirya zamu tafi Umarah!

Sannan game da Sarkin Kano, Mai Martaba Malam Muhammadu Sanusi II, wallahi, wallahi, wallahi ban taba zuwa fadar sa ba sai sau daya. Kai kusan ince ma wannan lokacin shine na farkon haduwa ta dashi gaba-da-gaba. Kuma dalilin wannan haduwar, mun ziyarce shine a kungiyance, a karkashin wasu manyan mu, da muke cikin wani group na WhatsApp, muka kai masa ziyara, muka gaishe da shi. Ban da wannan, wallahi ban taba kai wa Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II wata ziyara ta kashin kai na ba! Kuma Allah shine shaida. Kuma shi Sarkin yana nan raye!

Saboda haka, wadancan ‘yan siyasa, na shaida masu cewa, su bar kudin su, bana bukata, domin ni ina yin rubutu ne don abu uku:

1. Kare mutuncin addini na, gwargwadon iyawa ta. Kuma ko da zan mutu, na yarda inyi shahada wurin kare shi, babu-gudu-babu-ja-da-baya! Wanda ni a fahimtata, da fahimtar dukkan wani mai hankali, mai tunani, mai hangen nesa, kare Masarautun mu, wallahi kare mutuncin addini ne! Domin ko kai waye, duk iya yin ka, duk salon ka, baka isa ka raba addinin mu da masarautun mu ba!

2. Kare mutumcin yankin mu na arewa. Domin nayi imani da Allah, duk inda mutum ya tafi, kasar waje ne ko kudancin Najeriya, nasan cewa indai shi dan arewa ne na asali, to zaka tarar yana kishin yankin sa na arewa. Sannan ba zai taba yarda da sunan siyasa, azo ana neman a rusa su kuma yayi shiru ba. Kuma nasan cewa, idan ka cire Sarakuna, ko ka wulakanta muna su, ko ka raina su,to meye ya rage a arewar? Duk ‘yan siyasar nan da zaka ji wai da sunan siyasa, suna kokarin cin mutuncin wani mai sarauta, zaka tarar sun jahilci tarihi, kuma sun jahilci addinin su da al’adunsu ne! Kuma wawayen basu sani ba, suna yin kirari ne su daba wa cikin su wuka. Domin misali, kaci mutuncin addinin ka da al’adar ka, amma a daya gefen makiyanka da abokan zaman ka suna yi maka dariya, anyi ba’ayi ba kenan!

3. Kare mutuncin al’adun mu, tarihin mu da manyan mu. Domin duk al’ummar da ta yarda ana yi mata wasa da tarihi da al’adarta da bata sabawa addini ba da manyan ta; ko wani dan siyasa yazo yana neman ya rusa mata tarihi da sunan adawar siyasa, ko son zuciya, kuma tayi shiru, to bata san abin da take yi ba.

Don haka sai na basu hakuri, nace su rike kudinsu da duk abinda suka ce zasu bani, bana bukata, kuma rubutu akan bayyanawa mutane gaskiya, yanzu muka fara, kuma ba zan daina ba, babu-gudu-babu-ja-da-baya! Sanadiyyar haka, a wancan lokaci, lokacin Shugaba Jonathan, aka saka ni a gaba, wallahi sai da nayi wata uku bana kwana a gida na sosai. Kuma rubutun da nike yi a Facebook, aka ce dani in daina ko a dauki mataki a kaina, shima nace babu maganar in daina. Sanadiyyar haka aka yi hacking din Facebook account di na, na daina amfani da shi, kafin yanzu daga baya in bude wani sabo.

Ya ku ‘yan uwa, na kawo wannan bayanin ne ba domin komai ba sai domin mamakin wadancan ‘yan siyasar, magoya bayan Gwamna Ganduje, da suka kira ni, suke cewa wai Sarki yana bani kudi. Don su san cewa mu ba don kudi muke yi ba, a’a, tsakanin mu da Allah muke yi, da kuma kokarin wargaza tunani da shirin duk wasu makiya addinin Allah, makiya arewa kuma makiya masarautun mu. Kuma Alhamdulillahi, al’ummah ta fahimci hakan, sai dai ‘yan tsiraru, cikin cokali!

Sannan wai suna maganar Sanata Kwankwaso. Shine nace da su, ni wallahi, Allah shine shaida, ban taba sani ko haduwa da Kwankwaso ba. Kai watakila ma ni yanzu haka bai sanni ba, domin ban taba wata hulda, ta kusa ko ta nesa da shi ba. Watakila kawai ra’ayin mu yazo daya dashi akan maganar girmama Sarakunan mu da masarautun mu, wannan kuwa ba fashi da yardar Allah!

Saboda haka, wannan shine gaskiyar magana. Amma ba dole bane makiya su amince. Domin ba yardar su muke nema ba, yardar Allah muke nema a koda yaushe cikin al’amurran mu!

Sannan har kullun mu, abin tambayar mu anan shine: wai shin me yasa wadannan ‘yan siyasar marasa kishin arewa da kishin ‘yan arewa, suke da wannan mafarki na sai sun raba kan ‘yan arewa ta fuskar yin amfani da masarautu?

Sannan meye alakar wannan yunkuri na kikiro sabbin masarautu a Kano da makircin turawa a shekarun baya? Kuma meye alakar wannan yunkuri da kudurin turawan mulkin mallaka a yunkurin su na farko a shekarun 1905 zuwa 1914?

Sannan wace irin rawa bature Palmer ya taka wurin kirkirar tatsuniyar Hausa Bakwai domin ya baiwa abokan sa damar rusa masarautun kasar Hausa, da kuma kirkirar na bogi?

Anya kuwa ba wannan tatsuniyar bace wasu jahilan ‘yan siyasar nan ke amfani da ita ba, a matsayin hujja, ta su kirkiro sabbin masarautun bogi a Kano ba?

Wallahi ya zama wajibi wurin dukkanin ‘yan arewa na asali, ba bakin haure ba, wurin Kanawa na asali, ba bakin haure ba, suyi tunani, suyi karatun ta-natsu, su san cewa yaki ne fa aka kawo masu, wani mummunan hari ne fa aka kawo masu, shi yasa ake son ayi amfani da wasu daga cikin rubabbun ‘yan siyasar mu a ci mu da yaki.

Kuma wajibi ne mu fahimci cewa, fada da masarautar Kano fada ne da arewa baki-daya. Ba fada ne da Sarki Muhammadu Sanusi II kawai ba. Domin har kullun, kokarin makiya da magautan arewa shine, su nuna maku cewa, fadan na Sarki ne kawai. To wallahi ba haka bane. A masarautun arewa idan ka rusa ta Kano ai dole ne ya shafi sauran! Don haka mu kiyaye, mu zama a fadake koda yaushe, kar mu yarda ayi wasa da hankulan mu!

Ya kamata mu san cewa, wasu ne suke kokarin kifar da arewar mu. Kuma da karfin Allah, da buwayar sa ba zasu taba cin nasara ba. Domin Alhamdulillahi, mun riga mun gano su. Kuma ta Allah ba tasu ba!

Dama arewar yaya ta kare a halin yanzu? Ga abunda yake faruwa a Zamfara na ‘yan ta’adda barayi. Ga maganar Boko Haram da sauran matsaloli daban-daban. Kuma shine su wadannan miyagun suke so yanzu kuma su sake shirya wasu sabbin makirce-makirce ta hanyar jefa matsala a bangaren masarautun mu. Sai a wayi gari masaurautun mu sun lalace, har ya kai matsayin bamu ganin kimar su da girman su, shike nan su gama da mu. Allah ba zai basu nasara ba!

Yanzu misali, abun takaicin da yake faruwa a Jahar Kano, ana cewa za’a kashewa kowacce daga cikin wadannan sabbin masarautun na Ganduje kimanin kudi, wuri-na-gugar-wuri har Naira rabin biliyan; shin don Allah, Gwamnatin Jahar Kano bata ganin in ta zuba wadannan dimbin kudade a bangaren raya madatsun ruwan Jahar da suke kokarin kafewa, wato Dams, ba zai fi muhimmanci ba fiye da kashe su a bangaren kafa wasu sabbin masarautu da basu da wani tasiri wurin kakkabe dimbin talauci da yake damun kashi tamanin cikin dari na mutanen Jahar Kano?

Shin azuzuwan makarantu nawa ne Nairorin biliyoyin da Gwamna Ganduje zaya kashe domin raya wadannan sabbin masarautu marasa tasiri zata iya samarwa a makarantun Jahar Kano?

Don Allah, don Allah, don Allah ta yaya kafa masarautun da basu da mazauni a dokar kasa, masarautun da yanzu haka kotu ta rusa su, masarautun da basu da mazauni da asali a tarihin Jihadin Shehu Usman Dan Fodio, zasu iya magance dimbin talauci da fatara a tsakanin al’ummah? Shin idan an zuba wannan kudade a cikin harkar aikin gona, mutum miliyan nawa ne za’a samarwa aikin yi a wannan fanni?

Ya ku ‘yan uwa na masu daraja, wallahi ya zama wajibi muyi wa kan mu adalci. Don Allah mu dubi irin taimako da gudummawa da agaji da Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II, yake ba wa marasa lafiya a asibitocin Jahar Kano! Mu dubi irin agajin kayan abinci da yake rabawa masu azumi! Mu kalli kayan Sallah da yake rabawa mabukata, gajiyayyu talakawa, maza da mata! Haba, ko don wannan ba zai sa muci gaba da yiwa bawan Allah nan addu’a ba?

Ku sani, wadannan sabbin Sarakuna da Gwamna Ganduje ya kirkiro, a doka ba Sarakuna bane! Kotu ta tabbatar da cewa bata san da su ba. A Kano Sarki daya ne ake da shi, shine: Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II. Shine kadai Sarkin da Majalisar Sarakunan Najeriya suka sani. Kuma shine kadai Sarkin da Majalisar Sarakunan arewa suka sani, haka shine kadai Sarkin da Majalisar koli ta harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya suka sani; duk wanda bashi ba, ba Sarki bane; kuma sandar da aka basu ba sanda bace kokara ce! Ya kamata kowa yasan da wannan!

Sarkin Kano, Mai Martaba Malam Muhammadu Sanusi II, shine kadai Sarkin da ilahirin Kanawa suka yiwa mubaya’ah. Duk wanda bashi ba, wallahi sojan gona ne, wanda yayi shigar burtu yana so ya cuci Kanawa. Kuma duk matakin da Kanawa suka dauka a kansa, ya sani, shine ya jawo wa kansa.

Ya ku jama’ah! Irin gudummawar da Sarakuna, iyayen mu suke bayar wa a kasar nan, ta fuskar tsaro da zaman lafiya da yin sulhu tsakanin mutane da taimakon gajiyayyu, akwai wani dan siyasa da ya isa ya bayar da ita? Ko don kun ga cewa bature, arne, azzalumi, macuci ya kwace masu karfi, ya zamanto basu da kudi, basu da makamai da jami’an tsaro da gidan yari a hannun su, shi yasa kuke kokarin raina su da ci masu mutunci? Kuke kokarin karasa aikin bature? To wallahi baku isa ba, kun yi kadan! Sarakunan mu masu girma ne, masu daraja ne, kuma masu mutunci ne!

Har kullun, tsakanin mu dasu, tun daga kan Sarkin Musulmi har karamin Sarki na kasan-kasan sa, sai addu’a! Allah ya taimake su, Allah ya ja kwanansu, Allah yaci gaba da kare muna su, Allah ya kara masu Martaba da imani, amin.

Wassalamu Alaikum,

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jahar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun Imam ta adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma +2348038289761.

Share.

game da Author