An zabi Sanata Lawan Ahmed a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa zango na 9.
Lawal ya kayar da abokin takarar sa, Sanata Ali Ndume daga jihar Barno, inda ya samu kuri’u 79, shi kuma Ndume ya samu 28 kacal.
An gudanar da zaben ne a zaman Majalisar Dattawan na farko a yau Talata.
An bayyana sanarwar zaben sa da karfe 12: 17, kuma aka rantsar da shi da karfe 12:19.
Mohammed Sani-Omolori ne ya bayyana sakamakon zaben da kuma bayyana Lawan sabon shugaban majalisar.
Sanatoci 107 ne suka jefa kuri’a a zaben.
Dama tun da farko Sanata Lawan ne aka sa ran zai yi nasara, ganin yadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da dukkan sauran shugabannin APC da gwamnonin jihohi na APC ke goyon bayan sa.
Idan za a iya tunawa, Lawan ya yi takara a 2015, kuma shi APC ta so ya ci zabe a lokacin, amma Bukola Saraki ya kayar da shi, bayan ya hada kai da sanatocin PDP.
Daidai lokacin da ake rubuta wannan labari, ana kada kuri’ar zaben Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.
Ana fafatawa ne tsakanin Sanata Ovie Omo-Agege na APC da kuma Sanata Ike Ekwaremadu na PDP.