Wata mata mai suna Suliyat Toriola mai shekaru 28 ta bayyana a kotu cewa ba za ta amince mijinta ya sake ta ba sai fa idan shima zai dawo mata da budurcin ta.
Suliyat da mijinta Lateef sun shafe shekaru biyu kenan a aure.
Lateef ya nemi kotu ta raba aurenshi da Suliyat saboda tozarta shi da cin mutuncin sa da ta ke yi kullum.
“Babu ranar da Suliyat ba za ta ci mani mutunci na ba kuma a gaban koma waye.
Lateef yace a dalilin haka ya tattara kayansa ya bar mata gidan.
“Ina rokon kotu da ta warware auren dake tsakanina da Suliyat saboda na gaji haka nan.
Ita ko Suliyat ta ce Lateef matsafi ne domin sai da ya yi mata asiri kafin ya iya auren ta.
“Lateef ba namijin da zan gani haka kawai in ce wai ina so ya zama mijina ba ne. Mun hadu ne da naje gidan sa neman maganin kasuwa, anan muka hadu.
“ Lateef ya bukaci in kawo gashin gaba na sannan ya kwana da ni domin hada asirin. Bayan hakan ya faru an hada mini asirin sai daga baya kuma naji idan bashi ba rijiya. A haka muka yi aure.
Suliyat ta ce bayan ta auri Lateef sai ta fara rashin lafiya da hakan yasa ta fice daga gidan sa.
Alkalin kotun Raheem Adelodun ya daga shari’ar har sai Suliyat ta samu lafiya.
Ya kuma umurci ‘yan uwan ma’auratan da su gaggauta kai Suliyat asibiti domin likita ya duba ta sannan duk bayan kwanaki 15 su sanar da kotun halin da take ciki.