Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya maida wa Gwamnan Jihar Kaduna kakkausan raddi, dangane da wata gwasalewa da shi gwamnan ya yi masa.
Gwamna El-Rufai ya shiga shafin sa na soshiyal midiya, inda ya rika gwasale Sule da Hunkuyi cewa ya yi musu ritayar siyasa, yanzu ba su kara wani katabus.
Idan za a iya tunawa, Shehu Sani da Sanata Hunkuyi sun sha kaye daga ‘yan takarar jam’iyyar APC.
Sai dai kuma a bisa dukkan alamu wannan rubutu na gwamnan ya yi wa Shehu Sani ciwo, har ya maida masa kakkausan raddi A shafin san a Facebook:
“Ba za ka iya tutiyar cewa ka yi wa wani ritaya a siyasa ba, alhali gaba dayan siyasar ka, kai ka dogara ne da Buhari wajen cimma burin ka na siyasa.
“Har yau ba ka nuna jarumtar siyasar kaba, domin ba ka iya tsayawa da kafafun ka. Kokarin ka na neman zama Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa da ka yi kwanan nan ma bai yi nasara ba.
“Ka kafa tahirin tsilla-tsilla daga wannan ubangida, bayan kun bata kuma ka koma kan wancan ubangida. Kuma na yi amanna cewa shi ma Shugaba Muhammadu Buhari din sai yayi da na sani da kai. Na gaya wa Oshiomhole da Tinubu haka. Gashi tun kafin a yi wani nisa ka fara. Mai hali baya barin halin sa.
“Ba kai kadai ba ne ka fara ‘sake yin nasara’ a zabe, kuma ba kai ne za ka kasance na karshe ba. Gwamna Makarfi ya sake lashe zabe, kuma shi babu ma wanda ya kalubalanci nasarar ta sa a kotu cewa da harkalla ya sake cin zabe.”
Har ila yau, Sani ya ce El-Rufai ya rika kai gwauro ya na kai mari a wajen Buhari da kuma Shugaban APC Adams Oshiomhole domin ganin an biya masa bukatar sa ta kayar da su Sani din.
Daga nan kuma ya ce Buhari na da tunanin gane cewa abin da shi gwamnan ke fada a gaban sa daban, wanda ya ke fada a bayan idon sa ma daban.
Ya kuma sake tunatar da barazanar da ya ce Gwamna El-Rufai ya yi musu da kuma yadda ya ingiza magoya bayan sa a kan taba lafiyar su.
Daga nan kuma sai ya nuna cewa El-Rufai na jin haushin gajartar sa ce, inda Sanata Sani ya ce:
“Allah ne ya yi ka guntu, ba ni na guntule ka ba.”
A na sa bangaren Sanata Sani ya yi tutiyar cewa bai taba raba wa masu zabe kudi ba, kuma bait aba raba musu aatamfofi ba, bai kuma taba raba kan mutane domin ya ci zabe kamar yadda El-Rufai ya yi ba.
Ya kuma ce mulki ne dai gwamnan ya ke tutiya da shi, kuma zai sauka ya bari wata rana.
Discussion about this post