Jami’an Sintirin ‘Civil Defence’ (NSCDC) a Jihar Barno sun bada sanarwar damke Aliyu Mohammed, wanda ake zargi da yi wa Boko Haram safarar kayayyakin harhada bama-bamai a Maiduguri.
Babban Kwamandan su mai suna Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana haka a lokacin da ake tattaunawa da shi.
Ya ce wanda aka kama din mai shekaru 24, an kama shi ne tun a ranar 25 Ga Afrilu, bayan an samu rahotannin bayanai na sirri cewa ya na kan hanyar sa ne domin kai tarkacen harhada bama-bamai ga Boko Haram.
Binciken farko da jami’an suka yi, sun tabbatar da cewa Aliyu na kai wa Bokon Haram batiran wayar hannu, agoguna, kwamfutocin hannu, wato laptop da kuma tarkacen harhada bama-bamai, wanda suke hadawa su na yin mummunar barna.
“Wanda ake zargin wanda ke zirga-zirga a cikin Maiduguri a matsayin direban Keke NAPEP, ya aiwatar musu da wannan aika-aika sau da dama.
“An kuma same shi ya na da asusun ajiyar kudaden da Boko Haram ke aiko masa ya na sai musu kayayyaki a cikin watanni shida zuwa yanzu.
“An sha turo masa da makudan kudade daga Chad ta hanyar asusun ajiyar wani, maimakon a rika turo masa kai-tsaye a na sa asusun, wai don kada a gane shi.
Mohammed ya ce wanda ake zargin shi da wasu abokan sa sun sha kai hare-hare a masallatai da kasuwannin Maiduguri ba sau daya ba.