Shekaru bakwai bayan rasuwar Sanata Usman Al-Bashir, rikicin rabon gado ya tirnike a cikin iyalan da mamacin ya bari.
Al-Bashir ya rasu ne sakamakon hatsarin mota a kan hanyar Kano zuwa Zari’a, a ranar 2 Yuni, 2012.
Wani mai bayar da shaida a kotu a yau Laraba, mai suna Isa Bello, ya gabatar da shaidar cewa, Al-Bashir, wanda ya taba wakiltar Shiyyar Yobe ta Arewa a Majalisar Dattawa, ya rasu ya bar ‘ya’ya bakwai da mata daya.
Matar Al-Bashir ce ta shigar da kara a kotu cewa ta na rokon a raba gadon da mamacin ya bari, musamman wani katafaren rukunin gidajen sa.
Ta shigar da karar ce ta hannun lauyan ta mai suna Ayoola Oke, inda ta nemi kotu ta raba gadon kamar yadda shari’ar Musulunci ta gindaya.
Mai gabatar da shaida, Bello, wanda abokin marigayi Al-Bashir ne na kut-da-kut, ya shaida wa kotu cewa ya san Al-Bashir na da wasu gidaje guda bakwai a Abuja.
Da aka tambaye shi ko mamacin na da wasu magada baya ga ‘ya’ya bakwai da ya sani, sai mai shaidar ya ce bai sani ba.
“Wadannan ‘ya’yan sa bakwai dai su kadai na sani, sai kuma matar sa wadda likita ce.
“Mamacin ko iyaye ba shi da su yanzu a raye, saboda sun mutu shekaru da suka wuce.
“Saboda haka ni ba ni da wata masaniya ko ya ta ba yin wasu iyalin.” Inji Bello.
Ya kara da cewa kanin Al-Bashir wanda shi ne ke kula da gidajen na sa a Abuja, ya damka kulawar su a hannun Cibiyar Sasanta Rigingimu da ke a karkashin Kotun Daukaka Kara ta Shari’ar Musulunci.
Ya yi karin bayanin cewa Sanata Al-Bashir shi ke da rukunin kamfanonin Savanna Group of Compamies.
Sai dai kuma lauyan wanda ake kara mai suna Mohammed Sani, ya nemi kotu da ta yi watsi da shaidar da abokin sanata Al-Bashir ya bayar.
Ya ce maganganun ko shaidar da ya bayar ba gaskiya ba ce, duk ji-ta-ji-ta ce.
Sai dai kuma Mai Shair’a Ado Muktar, ya amince da shaidar da Bello ya gabatar. Ya kara da cewa: “A bisa dokar shari’ar Musulunci, ana karbar shaida ko da ji-ta-ji-ta ce ko a batun rigimar gado, muddin shaidar ta yi daidai da bayanan da kotu ta rigaya ta binciko.”
Daga nan sai ya dage sauraron karar zuwa 1 Ga Yuli.