RASHIN TSARO: Za mu kori ‘batagarin Fulani’ daga yankin Yarabawa –Ooni na Ife

0

Babban basaraken kasar Yarabawa, Ooni na Ife, Adeyeye Ogunwusi, ya bayyana cewa su na nan su na shirye-shiryen fatattakar duk wasu batagarin Fulani makiyaya daga yankin Yarabawa baki daya.

Ya yi wannan bayani ne a jiya Laraba, a lokacin da ya karbi bakuncin Sarkin Borgu, Muhammad Dantoro (Kitoro IV).

Basaraken ya koka da yawan hare-haren da ya ce ana kaiwa a yankin tare da cewa a baya can ba su san da wannan hare-hare a yankunan su ba.

Cikin wata sanarwar da aka raba wa manema labarai, kakakin yada labarai na Fadar Oono na Ife, mai suna Moses Olafare, ya ce basaraken ya furta cewa:

“Mu na zaune da Fulani a yankunan mu. Amma wasu batagari daga cikin su sun zo su na neman mamaye mu. Don haka za mu fatattake su, domin mu samar wa yankin zaman lafiya.”

“Yanzu lokaci ya yi da za a tantanci tsaki da kuma tsakuwa, wato a tantance tsakanin Fulani masu son zaman lafiya da kuma batagarin cikin su.”

“Mu na bukatar al’ummar kasar nan baki daya a yi zaman lafiya. Ba mu son zama cikin fargaba. Dalili kenan mu ke da bukatar tuntubar junan mu sarakunan gargajiya, domin samun dauwammiyar hanyar magance wannan hare-hare da ake fama da shi.

“Duk wanda ya bude baki z aka ji ya ce Fulani ne ke addabar mu da hare-hare. To a gaskiya abin ya isa haka nan! Tilas mu raba tsaki da tsakuwa, domin samar wa kan mu zaman lafiya. Mu samu hanyar kawo karshen wannan hare-hare daga wadanda ba su neman kasar nan da zama lafiya, ko ma ‘yan wace kabila ce.”

A na sa jawabin, Sarkin Borgu ya ce ya na goyon bayan Ooni na Ife a kan shirin da ya ce su ke yi domin samar wa yankin su zaman lafiya.

Share.

game da Author