RASHIN TSARO: Birtaniya ta gargadi ‘yan kasar su kauracewa Jihohin Barno, Zamfara, Abia, Katsina da Kaduna

0

Ofishin Kula da Harkokin Kasashe Rainon Ingila na Birtaniya, (FCO), ya gargadi ’yan kasar kada su kuskura su je wasu jihohi da ta kebe a Najeriya.

Ofishin na FCO, wanda shi ne ke kare muradu da manufofin Birtaniya a Kasashe Rainon Ingila, shi ne kuma ke gabatar da shawarwari ga ‘yan kasar masu tafiya ko shiga kasashe daban-daban na rainon Ingila sai kuma uwa-uba gargadi a kan matsalar tsaron da kasashen ke ciki.

Su na bayar da shawarwarin da suka shafi tsaron lafiyar su, sharuddan shiga wadannan kasashe, gargadi ga matsafiyan su da kuma batutuwa dangane da matsayi ko yanayin kiwon lafiya a wadannan kasashe.

Rahoton da ofishin ya fitar a kan matsalar tsaro a ranar Litinin, Birtaniya ta lissafa jihohin da ’yan kasar ta za su kaurace wa sun hada da: Barno, Yobe, Adamawa, Gombe, Delta, Bayelsa, Rivers, Akwa Ibom da kuma kilomita 20 tsakanin kan iyakar Jihar Zamfara da Jamhuriyar Nijar.

Sannan kuma ta ce kada ‘yan kasar ta su je jihohin Bauchi, Zamfara, Kano, Kaduna, Jigawa, Katsina da Kogi.

“Akwai yiwuwar ’yan ta’adda za su jaraba sa’ar kai munanan hari a Najeriya. Wadannan hare-hare kuma duk a Yankin Arewa maso Gabas ake kai su. Sai kuma Yobe da wasu kananan hukumomin da suka hada kan iyaka da Barno da kuma Damaturu, sai Jihar Adamawa.”

Bayan yin wannan gargadin, Birtaniya ta kuma yi magana a kan garkuwa da mutane.

“Akwai barazana da fargabar yawaitar yin garkuwa da mutane. Saboda haka idan ka na aiki ko tafiya ta kama ka a inda Boko Haram ko ISWA ke kai hare-hare, musamman a Arewa maso Gabas, to ka rika kaffa-kaffa da masu ta’addanci ko garkuwa da mutane.

Daga nan sai FCO ta ja kunnen su cewa a ko da yaushe su rika bibiyar bayanan da ofshin ke fitarwa domin su san hali da wurare ko yankunan da ke da matsalar tsaro.

Share.

game da Author