RASHIN TSARO: An maida ’yan bautar kasa 350 daga Barno zuwa Kano

0

Kodinata na Hukumar Kula da Masu Bautar Kasa (NYSC) na jihar Kano, Ladan Baba, ya bayyana cewa an maida masu bautar kasa 350 zuwa Kano daga jihar Barno.

Ya ce a yanzu wadannan masu bautar kasa a Kano za su yi atisayen sati uku.

Baba ya bayyana haka ranar Alhamis a Kano, a Sansanin Masu Bautar Kasa da ke Karaye.

Ya yi bayanin ne a lokacin da ya ke rantsar da sabbin masu bautar kasa, wato NYSC su 2,259 na rukunin ‘B’ na 2019 da aka tura Jihar Kano dmin yin aikin horon shekara daya.

Ladan ya kara da cewa wadanda aka tura daga Barno zuwa Kano ya zama dole ne saboda matsalar tsaro da ake fama da ita a yankin Arewa maso Gabas.

Daga nan sai ya yi kira ga masu bautar kasa da aka tura Kano su jajirce wajen aiki tare da yin amfani da damar da suka samu wajen bauta wa kasar su ta haihuwa.

Ya yi musu bayanin cewa za a ba su horo na motsa jiki, laccoci, tarukan cudanya da jama’a wasanni da tsalle-tsalle da sauran su.

Ya ce dukkan wadannan tare da faretin da za a koyar da su, duk sun zama wajibi ne domin a cusa musu da’a da kishin kasa.

Share.

game da Author