An kashe akalla mutane 96 sannan aka yi garkuwa da wasu da dama a fadin kasar nan cikin makon jiya.
Akasarin wadanda aka kashe dai fararen hula ne, amma har akwai sojoji da ma jami’an wasu fannonin tsaro daban-daban.
Wadannan hare-hare sun faru ne a lokuta daban-daban a inda ake fama da matsalar tsaro a cikin kasar nan.
RANAR LAHADI
An kashe soja daya da da jami’an NSCDC biyu a wani farmaki da barayin danyen man fetur suka kai musu cikin Karamar Hukumar Tai, a Jihar Ribas.
Sai kuma Jihar Barno, inda Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar wato SEMA, ta tabbatar da kisan mutane 30 da ji wa 42 rauni, a lokacin da aka kai wani mummunan harin kunar-bakin-wake, a wani gidan kallon kwallo, a Karamar Hukumar Konduga.
Bama-bamai uku8 ne suka tashi da misalin karfe 8 na dare a ranar waccan Lahadi din.
Jami’ai sun ce nan take mutane 17 suka mutu, sauran 13 kuma sun mutu ne zuwa wayewar garin Litinin, saboda rashin kulawa da kuma magunguna.
Duk dai a ranar Lahadi, mutane 8 suka mutu, wasu kuma da dama suka ji raunuka, sakamakon wani hari da ake zargin wasu makiyaya sun kai a Jihar Taraba, waccan Lahadi da dare. Wadanda aka yi abin kan idon su da kuma yan sanda duk sun shaida haka.
A Jihar Edo kuma wasu yan bindiga ne suka yi garkuwa da Limamin Cocin Katolika, mai suna Isaac Agubi.
An sace shi a Karamar Hukumar Akoko-Edo wajen karfe 5 na yamma.
RANAR LITININ
Jami’an yan sanda a Jihar Kaduna sun tabbatar da bindige wasu mutane uku a Unguwar Rimi. An bindige su ne a Gundumar Chawai da ke cikin Karamar Hukumar Kauru.
An bindige Monday Yahaya, SAamson David da Ashimile Danladi misalin karfe 2:25 na dare.
A Riyom kuma an kashe mutane hudu da wani soja daya bayan wani hari da aka kai a wannan yanki na Jihar Filato, da ake zargin Fulani makiyaya ne suka kai harin.
KISAN DA BOKO HARAM SUKA YI WA SOJOJI
Akalla an kashe sojoji 28 yayin da Boko Haram suka yi wa wani sansanin soja takakkiya a Gajiram, cikin Karamar Hukumar Nganzai da ke jihar Barno.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa an turo sojoji daga Monguno wajen karfe 9 na dare suka je suka kwaso gawarwakin wadanda aka kashe.
RANAR TALATA
An yi garkuwa da dan tsohon ministan kiwon lafiya, Isaac Adewole a jihar Oyo.
An yi garkuwa da Dayo Adewole a gonar sa da ke Iroko, kusa da Fiditi a Karamar Hukumar Afijio wajejen karfe 6 na yamma.
An arce da shi zuwa wani boyayyen wuri, amma aka sako shi a ranar Laraba.
An kuma yi wa wani malami na Jami’ar Jihar Ribas kisan-gilla. Wasu mahara ne suka kashe Emmauel Amadi.
Jami’an yan sanda a Ribas sun tabbatar da kisan wanda aka yi wajen 8 na dare a Rumuolumeni, cikin Karamar Hukumar Obio/Akpor.
A jihar Jigawa, wasu mahara sun dirar wa al’ummar Fachawa cikin Karamar Hukumar Ringim, har suka kashe wani dan bijilante.
Sun dira garin a kan babura wajen karfe 11 na dare, suka yi wa gidajen mutane kaca-kaca.
Sun yi zargin wannan dan bijilante din ne ya ja zugar yan sanda aka kama wasu yan uwan su.
RANAR ALHAMIS
Sarkin Tsafe, Muhammadu Bawa, ya ce mahara sun kashe mutane 18 a cikin yankunan Karamar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.
Ya ce mahara sun kai farmaki a kauyukan Bamamu, Danmale da Sako wajen yammacin Alhamis.
Sun dira kauyukan a kan babura kimanin 50.