Duk da cewa sama da kashi 80 bisa 100 na mazauna jihar Jigawa manoma ne gwamnatin jihar bata iya ware isassun kudade ba domin inganta aiyukkan noma a jihar, wato manoma na dandana kudar su.
Gwamnatin jihar ta na yi wa mutanen jihar romon bakin cewa za ta fadada aiyukkan noma a jihar amma har yanzu shuru kake ji.
Bisa ga yadda gwamnatin ke ware kudade a kasafin kudinta a tsawon shekara uku da suka gabata ya nuna cewa fannin noma baya cikin fanonnin da gwamnatin ke shirin ingantawa.
Wasu kwararru a fannin noma sun bayyana cewa da alamun cewa badi za a yi fama da karancin abinci idan gwamnati bata karkato da hankulanta ba wajen inganta fannin noma a jihar ba.
A kasafin kudi 2019 gwamnati ta ware Naira biliyan 160.1 domin fannin noma amma Naira biliyan 8.67 ne kawai ya isa fannin.
A 2018 gwamnati ta ware Naira biliyan 10.1 amma Naira biliyan 3.06 ta bada. A 2017 an kashe Naira biliyan 4.4 daga cikin Naira biliyan 6.3 din da aka ware.
Sannan a 2016 gwamnati ta ce ta ware Naira biliyan 8.6 billion amma Naira biliyan 1.5 ne kawai aka saki.
A shekarar bara manoma sun yi fama da ambaliyar ruwa da ya ci gonaki da dama a jihar sannan har yanzu gwamnati bata iat kasa tallafa wa manoma balle har ta dauki matakan da za su taimaka wajen hana aukuwar ambaliyar nan gaba.
A yanzu haka noma abincin da mutane za su ci a jihar jigawa da Najeriya gaba daya ya rataya a kafadun manoma talakawa ne, kuma suma din suna fama da karancin kayan noma kamar su taki, kayan zamani da sauransu.
Malamin koyar da aiyukkan noma a jami’ar gwamnatin tarayya dake Dutse Ado Nasir yace kamata ya yi gwamnati ta samar da gona kamar hekta 300 domin noman ranni.
“Banda samar da abinci da wannan hakan zai yi, matasa za su samu aikin yi a fadin jihar da akasa baki daya.
Nasir ya kuma ce samar da kayan aiyukkan noma kamar su takin zamani, ingantattaun irin shuki da magungunan feshi na da matukar mahimmanci.
“A yanzu dai jihar Jigawa na fama da karancin ma’aikata da suka kware wajen noman zamani da za su rika koyar da manoma a jihar.
Kakakin ma’aikatar aiyukkan noma Zubairu Suleiman ya bayyana cewa gwamnati ta dauki matakan inganta aiyukkan noma a jihar kamar haka:
1. Samar da kananan na’urorin girbin amfanin gona guda 300 domin raba wa manoma da shigo da shirin daukan matasa domin noman gaiya.
2. Gwamnati ta samar da gona dake da fadin hekta 500 domin noman shinkafa a kananan hukumomin Miga da Kaugama sannan ta dauki matasa 1,000 da za su noma gonar.
3. An inganta kamfanin kera kayan aiyukkan noma na jihar (JASCO) domin samar da kayan aiki.
GA YADDA GWAMNATI TA KASA KUDADEN DA TA WARE WA AIYUKKAN NOMA.
1. Za a yi amfani da Naira miliyan 10 domin siyo ingantattun irin shuka.
2. An ware Naira miliyan 8.5 domin binciken ingantattun irin shuka.
3. Yin amfani da Naira miliyan 10 domin horar da kwararrun ma’aikatan fadada aiyukkan noma da manoma 450 kan dabarun zamanin 450.
4. Gwamnati ta ware Naira miliyan 55 domin shirin na noman gayya ga matasa da kuma samar da takin zamani,irin da magungunan feshi.