Ranar Litini a Abuja ne Kungiyar (PEPFAR) dake yaki da hana yaduwar cutar Kanjamau ta karama wasu ‘Yan Najeriya 16.
PEPFAR ta karama wadannan mutane ne bisa ga gudunmawar da suka bada a yakin hana yaduwar da cutar kanjamau a Najeriya.
Shugaban hukumar hana yaduwar cutar kanjamau ta kasa (NACA) Sani Aliyu kuma daya daga cikin wadanda aka karrama ya bayyana cewa girmammasu da PEPFAR ta yi dama ce domin kara zage damtse a yaki da kawar da cutar a kasar nan.
Aliyu ya yi kira ga hukumomin kawar da cutar da sauran mutane dasu hada hannu da gwamnati domin ganin an hana yaduwar cutar sannan da nuna wa duk kungiyoyin bada tallafi hanyoyin da zasu bi domin samun nasara a ayuukan da suka a gaba.
“ PEPFAR itace kungiyar da ke tallafa wa Najeriya daga kasar Amurka wajen kawar da kanjamau. Sannan a shekaru 15 da suka gabata kungiyar ta tallafa wa kasar da dalla miliyan 400 duk shekara.
“ Tallafin PEPFAR na samar da magunguna wa kashi 80 bisa 100 na mutanen dake dauke da cutar a kasar nan.
Da yake jinjina kokarin da mutanen da aka karama din jakadan kasar Amurka a Najeriya Stuart Symington ya yi kira ga duk bangarorin kasan kan hada hannu da gwamnati domin ganin an samu nasara wajen kawar da cutar.
Tobore Ovuorie dan jarida kuma mai gudanar da bincike da Alban Anonyuo mai rajin kare hakkin dan Adam kuma shugaban kungiyar kare cin zarafin yara sun ce a dalilin wannan girmamawar da suka samu za su kara maida hankali wajen an samu nasara abin da aka sa a gaba.