Oshiomhole baya tauna magana kafin yayi, ba zai iya rike jam’iyyar APC ba – Inji Oyegun

0

Tsohon shugaban jam’iyyar APC, John Oyegun ya soki shugaban jam’iyyar APC Adam Oshiomhole da kakkausar murya cewa Kadifirin sa yayi yawa sanna ga zaro magana yadda yaga dama ba abinda ya dame shi.

Wannan shine karo na farko da tsohon shugaban jam’iyyar Oyegun zai fadi wani abu game da shugabancin Oshiomhole.

” Ace wai mutum bashi da linzami a baka, duk yadda yaga dama zai labto magana babu taunawa. Ai ba haka ake shugabancin jam’iyya ba. Gashi duk ya rikirkita jam’iyyar tana neman ta tarwatse.”

Idan ba a manta ba a Kwanakin baya ne mataimakin jam’iyyar na yankin Arewa, Lawali shu’aibu ya yi kira ga shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole da ya sauka daga kujerar shugabancin jam’iyyar.

A wannan karon ma Oyegun ya bi sahun sa inda ya kara da cewa, duka matsalolin da aka samu a jihohin da APC ta fadi zabe Oshiomholen ne ya yi sanadiyyar haka.

” Ba a bari wa jiha ta yi gaban kanta wajen zaben fidda gwani idan har ana so ayi nasara. Dole sai uwar jam’iyya ta saka ido ta kuma ba kowa hakkin sa idan har ana so a yi nasara.

” Amma shi Oshiomhole da yake ba kwararre bane wajen iya jagorancin jam’iyya duk ya tarwatsa jam’iyyar. Maimakon ya nemi hadin kan kowa da kowa ne, Oshiomhole rarraba kan ‘yan jam’iyyar yake yi.

Jaridar Punch ce ta wallafa wannan hira da Oyegun.

Share.

game da Author