Nine nafi cancanta Buhari ya nada ministan man Fetur – Guru Maharaji

0

Shugaban majami’ar bauta na Guru Maharaji, Sat Guru Maharaji ya ce shine ya fi dacewa shugaban Kasa ya nada sabon ministan albarkjatun man fetur.

Maharaji dai shine shugaban majami’ar bauta na ‘One Love Family’ sannan ya kara da cewa duk sauran addinai sun gaza saboda haka shine zai iya rike ire-iren wadannan ma’aikatu a kasar nan kuma a samu ci gaban da aka dade ana nema a samu.

Baya ga wannan ma’aikata ya ce zai so ace idan Buhari ya tashi nadashi ya hada masa da ma’aikatun Ruwa da na Ayyukan Gona.

Yace shine fa kawai mafita ga matsalolin da ake samu a kasar nan. Sannan kuma ya ce lallai a kara mai da hankala wajen samar wa talakawa ababen more rayuwa da kuma tallafi. Kuma yayi kira da a samar wa Alkalan kasar nan albashi mai tsoka domin gujewa cika aljuhu da rashawa.

Maharaji ya ce muddun aka amida hankali ga haka toh, tabbas za a samu ci gaba matuka.

Share.

game da Author