Ni ba lalatacce bane kuma zan garzaya kotu – Limamin Cocin COZA

0

Babban Limamin Cocin Commonwealth of Zion Assembly, wanda aka fi sani da COZA, Abiodun Fatayinbo, ya karyata zargin yi wa matar fitaccen mawaki Timi Dakolo fyade.

Fatoyinbo yace karya Busola Dakolo ke yi masa da kuma sharri

A cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Juma’a, pasto Fatoyinbo ya ce, “ban taba yin fyade ba a rayuwa ta.”

Ya ce karya ce kawai da karairayi ake yi masa.

“Ku dubi irin shaharar da ta yi da shaharar da mijin ta ya yi. amma ta fito a duniya ta furta wannan kazafi a kai na. A gaskiya na yi mamaki kwarai. Na ma kasa cewa komai.

Busola ita ce mace mashahuriya ta biyu da ta fito ta ce Fatoyinbo ya yi mata fyade. Ta farkon ita ce Ese Walter.

Busola ta fito karara a cikin wata tattaunawa da YNaija ta yi da ita ta bayyana wannan zargi karara.

Chude Jideonwo ne yay i tattaunawar da ita, kuma aka watsa bidiyon a soshiyal midiya kowa ya kalla kuma ya saurara.

Busola ta ce abin ya faru a shekarun baya ne, lokacin ko shekaru 18 ba ta kai ba. Fasto Fatoyinbo ya kai ziyara gidan su, kuma ya yi mata fyade a gida.

Ta ce a baya ta na zuwa ibada ne a cocin sa. Amma da ya kai ga yi mata fyade, sai ta janye jiki, ta daina zuwa kawai.

Ta ce duk shugabannin cocin sun san da rigimar, amma sai suka yi kokari suka danne maganar ba ta ita fili ba a lokacin.

Shi kuma limamin cocin Fatayinbo, sai ya roki iyayen ta suka yafe masa. Ya ce shaidan ne ya ribbace shi.

Wannan zargi dai ya janyo fushi kuma ya harzuka jama’a da dama tun daga jiya Juma’a bayan buga tattaunawa da Busola da aka yi.

Jama’a da daman a ta yin kira da a kama Fatayinbo a gurfanar da shi kotu.

Fatoyinbo ya tabbatar da cewa ya san Busola kuma ya san iyayen ta tun shekarun baya can a Ilorin a farkon lokacin da ya kafa cocin sa, cikin 1999.

Sai dai kuma ya ce idan baya ga harkokin coci da yi mata addu’o’i, babu abin da ya taba hada shi ko ya taba shiga tsakanin sa da Busola.

A gefe daya kuma, fitattun mawaka irin su Don Jazzy, Toke Makinwa, Daddy Freeze da sauran su da dama, sun jinjina wa Busola da har ta fito ta bayyana abin da ke cikin zuciyar ta.

Sai dai kuma tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, wato Reno Omokri, ya fito ya kushe Busola, tare da cewa Fatoyinbo ba zai taba zubar da girman sa ya yi wa karamar yarinya fyade ba.

Duk da ya ce ba ya son limamin na Cocin COZA, amma kuma ya na tababar zancen da Busola ta yi masa zargi.

Sai dai kuma dimbin wadanda suka rika kiran a gaggauta hukunta faston, sun tafi a kan ra’ayin cewa ‘lalatacce dai lalatacce ne, ko a gidan wa ya ke.’

Yadda limamin Cocin COZA ya danne ni da karfin tsiya

Matar fitaccen mawakin nan mai suna Timi Dakolo, ta bayyana yadda babban limamin Cocin COZA, mai suna Biodun Fatoyinbo ya danne ta da karfin tsiya, ya yi mata fyade.

An sha tsoma sunan Fatoyinbo cikin harkallar badala da matan aure da ma wadanda ba na aure ba, masu zuwa cocin sa.

Shi da matar sa mai suna Modele suke tafiyar da cocin na sa.

Busola ta fito ta fallasa wannan zargi ne a cikin wata hira da YNaija, tare da Chude Jideonwo, kuma aka watsa a soshiyal midiya jiya Juma’a.

Wannan tattaunawa ta zama kamar gobarar daji, inda ko’ina a kasar nan labarin ake ta yi.

Ta ce abin ya faru a kafin ta daina zuwa cocin sa, kuma sau biyu ne ya yi lalata da ita a cikin mako daya.

Ta ce a karon farko ya je ne har gida ya same ta, da ya ke ya na zuwa wurin iyayen ta. A karo na biyu kuma a kan hanya ne suka hadu, ya ratse da ita ya yi mata fyade.

Ta ce bayan ya yi mata fyade, ya furta cewa, “Ke ai sai ma ki gode wa ubangiji, tunda limamin coci ne kuma makusancin ubangiji ya yi miki fyade.

Share.

game da Author