Neymar ya musanta zargin Fyade

0

Fitaccen dan wasan kwallon kafa dan kasar Brazil, Neymar Jnr, ya karyata zargin fyade da ake masa wai yayi wa wata ‘yar kasar Faransa a wani Otel.

Lauyoyin Neymar sun karyata wannan zargi inda suka ce abin bita-da-kulli ne kawai amma babu kamshin gaskiya a ciki.

Idan ba a manta ba tun bayan sallama da yayi da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Neymar ya kasa yin wanin azo agani a sabuwar kulob din sa wato PSG.

Yanzu dai alakalan wannan mata sun ce lallai Neymar ya aikata wannan mummunar abu domin kuwa kamar yadda ita matan ta ce Neymar ya danne ta da karfin tsiya domin ko da ya shigo Hotel din ya shigo a buge ne tatil da giya. ” Anan dai muka rungumi juna yana ta dan sasshafani. A haka kwatsam sai naji shi da karfin tsiya yana neman danneni. Ni kuma na tsorata har ya samu yi abin da yake so.

Neymar ya musanta wannan zargi.

Share.

game da Author