Neman ‘yar da zata kira ni Uwa, ya sa na sace jaririyar wata – Inji barauniyar jaririya

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta bayyana cewa ta kama matar da ta sace jaririya a asibitin koyarwa na jami’ar Filato JUTH.

Kwamishinan ‘yan sanda Isaac Akinmoyede ya sanar da haka inda ya kara da cewa rundunar ta yi nasaran kama Mrs Leritshimwa Diyal mai shekaru 32 bayan dagewar da suka yi wajen gudanar da bincike.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne asibitin JUTH ta shiga rudani inda da rana tsaka wata mata ta sace jaririya a asibitin.

Mary Chukwuebuka mazauniyar Zaramangada ta haifi jaririyarta a wannan asibiti inda bayan ta sauka lafiya Mrs Diyal ta sace jaririyar.

Mary ta ce wata mata sanye da rigar ma’aikatan jinya na asibitin ta zo ta dauki jaririyar da sunan yi wa jaririyar gwaji.

A takaice dai hankalin kowa a asibitin ya tashi bayan Mary ta jira na tsawon awa daya wannan ma’aikaciya bata dawo wa mata da jaririyarta ba.

Nan da nan Mary da mijinta suka shigar da kara ofishin ‘yan sanda wanda su kuma suka shiga bincike.

Akinmoyede ya bayyana cewa bayan sun kama Mrs Diyal sai ta yi musu karyan cewa ta haifi wannan jaririya ce a lokacin da take hannun masu garkuwa da mutane.

“ Ta bayyana cewa kafin masu garkuwan su kama ta ta kan je awon ciki a asibitin JUTH.

Akinmoyede ya ce bayan sun ci gaba da bincike ne Mrs Diyal ta fadi gaskiya cewa ta sace wannan jaririya ce daga wannan asibiti.

“ Diyal ta ce ta sace wannan jaririya ce domin ta sami dan da zai rika kiranta da sunnan uwa ganin cewa ta yi tsawon shekaru bakwai ba ta haihu ba.

Diyal ta ce ita da mijinta sun nemi taimako a duk inda suka sani amma ba su sami mafita ba sannan ta ce ta sace wannan jaririya ce ba tare da sanin mijinta ba.

Akinmoyede ya ce da zarar sun kammala gudanar da bincike za su maka Diyal kotu.

Share.

game da Author