Najeriya ce kasa ta biyu dake fama da matsalar yin bahaya a waje a duniya – UNICEF

0

Sakamakon binciken Asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ya nuna cewa a jerin kasashen duniya dake fama da matsalar yin bahaya a waje Najeriya ce ta biyu a Duniya.

Sauran kasashen duniya dake fama da wannan matsala sun hada da India, Ethiopia, Niger, Sudan, Chad, Mozambique, Indonesia, Pakistan da China.

Jami’in kungiyar WASH Bioye Ogunjobi ya sanar da haka a taron wayar da kan mutane game da ilollin yin bahaya a waje wanda UNICEF ta shirya a Ibadan.

Ogunjobi yace sakamakon binciken ya kara nuna cewa mutane miliyan 47 na yin bahaya a waje sannan wasu miliyan 32 na amfani da bandakunan da basu da tsafta.

Ya ce kwanakin baya WASH ta bayyana cewa daga cikin kananan hukumomi 774 dake kasar nan 13 ne kadai suka iya hana yin bahaya a waje.

Sannan a kwanakin baya kuma gwamnatin tarayya ta kafa dokar ta baci a wajen tsaftace muhalli domin kawar da matsalar yin bahaya a waje musamman jami’o’i, firamaye, kasuwani da tashar motoci a Najeriya.

Ogunjobi ya ce yin bahaya a waje na cutar da kiwon lafiyar mutane musamman yara ‘yan kasa da shekara biyar.

“Kamuwa da amai da gudawa, Hepatitis, zazzabin cizon sauro, ciwon hakarkari wato pneumonia na daga cikin cututtukan da akan kamu dasu idan ba a tsaftace muhalli.

Ogunjobi yace domin guje wa wannan matsala kamata ya yi gwamnati ta maida hankali wajen ganin ta kawar da matsalar.

“Tabas gwamnati baza ta iya gina wa kowa dakin ba haya ba amma idan aka maida hankali aka hannu da kungiyoyi za a samu nasara a akai.

Share.

game da Author