Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta kama kamfani dake sarrafa jabun zuma mai suna ‘Up The Rock Church of God’ a Durumi Abuja.
Shugaban hukumar Moji Adeyeye ta sanar da haka inda ta kara da cewa sun kama wannan kamfani a dalilin rashin yin rajista da hukumar da kuma yin amfani da wuri mara tsafta wajen sarrafa zuman da suke yi.
” Mun kama wannan kamfanin ne bayan wani ya tona asirin kamfanin a yanar gizo.
“Sannan binciken da muka gudanar akan wannan zuma ya tabbatar mana cewa zuman jabu ne da zai iya cutar da kiwon lafiyar mutane da dama a kasar nan.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne NAFDAC ta kama kwalaye 401 na abin sha da wa’adin amfanin su ya cika a Minna jihar Neja.
Jami’in hukumar Anikoh Ibrahim ya sanar da haka a wata takarda da ya rabawa manema labarai.
Ibrahim yace hukumar ta yi nasarar kama wadannan kwalaye bayan an tona asirin wani dan kasuwan dake boye da wadannan kaya a gidan ajiyan kaya da wasu mutane suka yi.
Ya ce gidan ajiyan kayan na bayan kasuwan Gwari dake karamar hukumar Chanchaga ne.
” Mun kama katan 376 na Amstel Malt, katan 17 na Coca-cola da katan takwas na Maltina.
Ibrahim yace bisa dokar hukumar bai kamata ‘yan kasuwa su ci gaba da ajiye kayan abincin da amfanin su ya kare ba.