Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta kasa (NAFDAC) ta bada umurnin hana siyar da maganin kashe kwari ‘Sniper’ a kasuwanin kasar nan.
NAFDAC ta dauki wannan mataki ne domin hana matasa kwankwadan ruwan maganin da a yanzu haka yake neman ya zama ruwan dare a kasar nan.
Wannan sanarwan ya fito ne bayan ‘yan kwanaki da hukumar ta bayyana cewa za ta hada hannu da wasu hukumomi a kasar nan domin ganin an rage siyar da wannan maganin a kasuwanin kasar.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne rahotannin yadda matasa dake karatu a jami’o’In kasar nan ke kwankwadan ruwan wannan maganin duniyar ta ishesu.
Shi dai wannan wannan magani wani kamfanin Najeriya da ta hada gwiwa da kamfanin kasar Swiss ne ke sarrafa shi domin kashe kwari a gonaki.
Bisa ga sharadin amfani da maganin sai an garwaya shi da ruwa ko kuma da kananzir kafin a yi amfani da shi a gona.
Matalar da ake fama da shi a kasar shine amincin wannan magani bai tsaya a kashe kwari ba domin mutane ma suna amfani da shi wajen kashe kawunan su.
Discussion about this post