Jiga-jigan Kungiyar Kare Muradin Siyasar Yarbawa Zalla (NADECO), sun bayyana cewa su na kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya bayyana sunan marigayi Cif MKO Abiola a matsayin shugaban kasa.
Sun kuma yi kira da kira kasaitaccen taron makomar Najeriya domin kamo bakin zaren yadda Najeriya za ta ci gaba.
Wadanda suka yi wannan kira, wadanda a cikin su har da tsohon gwamnan soja na Jihar Lagos, Ndubuisi Kanu, Amos Akingba da Ayo Opadokun, sun yi wannan kira ne a lokacin da suke ganawa da manema labarai a Lagos.
Da ya ke karanta takardar bayanin na su, Opadokun ya ce irin wannan taron zai kunshi shugabannin dukkan bangarorin kabilun kasar nan ba wai wasu wakilai da gwamnati za ta nada su wakilci jama’a ba.
“Mun yi wannan kira ne saboda kafin sojoji su fara mulki da karfin tsiya a kasar nan, cikin 1966, gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin yankuna su na da karfi sosai, kuma sun a biya wa al’ummomi dukkan bukatun da suka wajaba a biya musu.
Sun ce maida komai dungurugun a hannun gwamnatin tarayya da aka yi, ya haifar da cikas a wurare da dama.
“Akasarin jihohi a yanzu duk sun dogara ne da jiran kason kudade a duk karshen wata daga gwamnatin tarayya.
“Najeriya ta daina yaudarr kan ta da al’ummar cikin ta, ta na kiran kan ta fedaraliyya.” Inji Opadokun.
NADECO ta ce ta yi amanna ce wa komawa a kan Dokar Najeriya ta 1960, wadda ta damka albarkatun karkashin kasa na kowane yanki a yankin da arzikin ya ke, ita ce mafita domin kawo ci gaban kowane yanki a kasar nan.
Daga nan NADECO ta yi kira ga gwamnatin Najeriya ta gaggauta kawo karshen kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma satar shanu da rikice-rikicen Fulani da makiyaya a fadin kasar nan.
Daga nan sai NADECO ta yin kira da a gaggauta bayyana sunan Marigayi Mashood Abiola a matsayin shugaban kasa, duk kuwa da cewa ya rigaya ya mutu tuni.
Ta kuma nemi a samu wani katafaren gini na gwamnatin tarayya a sa masa sunan Abiola.
“Ba za mu yarda a maida shi wani gwarzo na yankin da ya fito kawai ba, ta hanyar sa wa Jami’ar Lagos sunan sa.
“Sannan kuma ita ma matar sa Alhaja Kudirat Abiola a ba ta wata lambar girmamawa ta musamman ta kasa, saboda shahadar da ta yi wajen tabbatar da cewa an kafa ingattaciyar dimokradiyya a Najeriya.”