Messi ya fi kowa daukar albashi a duniyar ‘yan wasa

0

Fitacciyar Mujallar nan da ake Forbes ta wallafa rahoton karin yawan albashin ‘yan wasa 100, inda ta ce Messi yana daukar dala miliyan 127 a duk shekara a yanzu.

Babban abokin hamayyarsa, wato Cristiano Ronaldo na kungiyar kwallon kafa ta Juventus ne ya zo na biyu. Ronaldo yana karbar dala Miliyan 109.

Neymar na kungiyar kwallon kafa ta PSG ne ke na uku a jerin attajiran ‘yan wasan. Yana karbar dala Miliyan 105.

Yar wasan Tanis, Serena Williams wadda ita ce kadai nace a jerin sunayen da aka wallafa kawai mace a cikin jerin sunayen da Forbes ta wallafa na karbar dala miliyan 29.

A shekarar da ta gabata dan wasan boxing, Floyd Mayweather ne ya fi kowa daukar albashi amma yanzu Leo Messi ya ajiye shi a gefe ya dare kan gaba.

Kamar yadda rahoton ya bayyana ‘yan wasan kasar Amurka ne suka fi yawan ‘yan wasan dake daukan albashi mai tsoka, daga ita sai ‘Yan wasan kasar Birtaniya da ke matsayi na biyu sai kuma ‘Yan wasan kasar Faransa da Spain da ke da ‘Yan wasa uku-uku.

Ga jerin 10 daga ciki

1. Lionel Messi $127m (£99.8m)

2. Cristiano Ronaldo $109m (£85.6m)

3. Neymar $105m (£82.5m)

4. Canelo Alvarez $94m (£73.8m)

5. Roger Federer $93.4m (£73.3)

6. Russell Wilson $89.5m (£70.3m)

7. Aaron Rodgers $89.3m £70.1m)

8. LeBron James $89m (£69.9m)

9. Stephen Curry $79.8m (£62.7m)

10, Kevin Durant $65.4m (£51.3m)

Jerin ‘yan wasa 100 da suka fi kudi

Share.

game da Author