Matawalle yayi arangama da Mahara a Zamfara

0

Mahara sun farwa tawagar sabon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle a hanyarsa ta zuwa kauyen Lilo, dake karamar hukumar shinkafi.

Wani ganau da ya tsokata wa PREMIUM TIMES ya ce maharan sun bude wa tawagar gwamnan ne adaidai gwamna matawalla na kokarin isa kauyen Lilo domin jajaen ta wa mutanen da aka kaiwa hari sannan da da dama suka rasa rayukan su.

Sai dai kuma jami’an tsaron dake tare da gwamna basu yi kasa-kasa ba domin suma sun bude wa maharan wuta inda cikin gaggawa suka waske da gwamnan sannan suka ci gaba da tafiyar su.

” Ba za mu iya tsayawa a wannan wuri ba domin su maharan suna can tsallaken rafi ne. ba za mu iya tunkaran su ba. a wannan lokaci. ” Haka wani jami’in dake tare da tawagar ya fadi.

Sai dai kuma mutane fadar gwamnati ta fitar da takarda cewa tawagar gwamnan ne ya fatattaki maharan a lokacin da suka yi kicibus da su a hanhyar su ta zuwa garin Lilo din.

” Mun yi kicibus da mahara a hanyar mu na zuwa kauyen Lilo, jami’an tsaron dake tawagar gwamna sun nuna bajinta matuka inda nan take suka far wa maharan suka fatattake su.

Sai dai kuma wasu da ke ganin wannan magana ba haka bane sun shaida mana cewa akwai sarkin Shinkafi, Shugaban Jam’iyyar PDP da wasu jiga-jigan gwamnatin jihar tare da gwamnan, ” tayaya za a ce wai ya farwa mahara tare da wadannan mutane?”

Share.

game da Author