Awoyi kafin a rufe majalisar jihar Kaduna ta 8, majalisar ta rattaba hannu a kudirin yi wa ayyukan addini katanga a jihar Kaduna.
Idan ba a manta ba anyi ta yin cece-kuce game da shirin gwamnatin jihar Kaduna na yi wa ayyukan addini iyaka a Kaduna.
Malaman addinin musulunci da na Kirista sun yi to tofa albarkacin bakin su da yin tir da shirin yi wa ayyukan addini iyaka a Kaduna.
Kakakin majalisar jihar, Aminu Shagali ne ya jagoranci wannan zama.
Ita dai wannan doka idan gwamna Nasir El-Rufai ya saka hannu zai yi wa ayyukan addini da ya hada da yin wa’azuzzuka iyaka.
1 – Za a kirkiro da ma’aikata da zata rika tantance wa’azuzzuka da kuma malaman da za su rika yin wa’azi a fadin jihar.
2 – Kowani malami sai ya mallaki lasisin yin wa’azi, musulmine ko Kirista.
3 – Za a kafa irin wadannan ofisoshi a kananan hukumomin jihar. Wadda sune za su rika mika wa hukumar sunayen malamai da Fastocin da za a tantance sannan kuma aba su lasisin yin wa’azi. Duk wanda bashi da lasisin yin wa’azi zai ko ga tasko.
4 – Daga yanzu sai dai ka saurari wa’azin ka a cikin mota, gida, cikin masallaci da da dakuna. Duk wanda aka kama ya kure wa’azi yana saurare zai kuka da kansa.
5 – Duk wanda ya kure karatu ko wa’azi ta lasifika daga karfe 11 na dare zuwa karfe 4 na safe zai yi kwanan kurkuku ko kuma ya biya taran naira 200,000.
6 – Sannan kuma duk wanda aka samu yana fadin kalamun batanci ga wani ko addini zai biya taran naira 100,000 ko kuma a garzaya da shi kurkuku ko kuma duka.
Shi dai wannan kudiri, gwamnatin Kaduna ta mika shi majalisar jiha tun a 2016.