MAJALISAR DATTAWA: Sanata Ndume ya ce ba zai janye wa Sanata Lawan ba

0

Sanata Ali Ndume ya bayana cewa har yanzu ya na cikin takarar Shugaban Majalisar Dattawa, duk kuwa da cewa abokin hamayyar takarar daya, Sanata Danjuma Goje ya janye wa Sanata Ahmed Lawan.

Ndume ya yi wannan bayanin jim kadan bayan da Sanata Goje ya bayyana janyewa ga Sanata Lawan, bayan sun ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari a Fadar Shugaban Kasa.

Goje ya ce ya janye ne duk kuwa da kiraye-kirayen da ake yi masa daga sassa daban-daban na fadin kasar nan cewa ya fito ya tsaya takarar.

Daga nan ya kara da cewa janyewar ta sa na daga girmama jam’iyyar APC da ya ke yi, tare da ganin jam’iyyar ta kara dinkewa wuri daya.

Sai dai kuma har yanzu shi Ndume ya na kan bakan sa cewa bai yarda uwar jam’iyya ta nada Lawan kai-tsaye, ba tare da an yi zabe ba.

Dalili kenan ya ce shi ma ya fito takara domin a kafsa da shi.

Shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole da jagoran APC, Bola Tinubu sun nemi Ndume da ya janye wa Lawan, amma ya tubure, ya ce sai an yi zabe.

A cikin sanarwar da Ndume ya fitar, ya ce ya yi murna da janyewar da Goje ya yi wa Lawan, domin a halin yanzu zaben ya rage tsakanin sa da Ahmed Lawan kenan.

“Yanzu ta rage wa sabbin zababbun sanatoci su yi zabi tsakanin wanda suka san zai yi wa kasar su aiki, da kuma wanda zai zama dan amshin-Shatan wasu gungun iyayen jam’iyya.”

A ranar 11 Ga Yuni za a kaddamar da Majalisar Dattawa Zango na 9, kuma a ranar za a zabi Shugaban Majalisar Dattawa.

Share.

game da Author