MAJALISAR DATTAWA: EFCC ta janye tuhumar Goje da take yi a kotu bisa zargin wawushe naira biliyan 25

0

Akalla hukumar EFFCC ta shafe sama da shekaru takwas tana tsikarar Goje, ana ta kai ruwa rana da lauyoyin sa da na hukumar amma sai gashi kwatsam duk da haka yau dai lauyoyin hukumar sun janye karar sun ce yanzu maganar ta koma ofishin Antoni Janar domin a ci gaba da ita.

Kamar yadda kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito ta ce ko da aka bukaci a saurari maganr a gaban Alkali Babatunde Qadri, na babban kotun tarayya dake garin Jos, sai lauyan EFCC yayi maza ya tashi ya ce maganan gaskiya sun hakura da ci gaba da bibiyar wannan shari’a, sun ma hakura hakanan.

Sai dai kuma daga baya Lauyan ofishin Antoni Janar ya bayyana a kotun inda ya nemi kogtun ta daga shari;ar har sai zuwa wani lokaci, domin ya samu daman shiryawa sosai.

Idan ba a manta ba sanata Danjuma Goje ya janye daga takarar zama shugaban majalisar dattawa bayan ganawa da shugaban kasa da gwamnan jihar Kaduna ya jagoranta da suka yi.

Goje yace ya janye wa Ahmad Lawan ne domin daraja shugaba Buhari da kuma bin umarnin jam’iyyar.

Share.

game da Author