Mahara sun farwa garin Rigasa dake karamar hukumar Igabi jihar Kaduna a cikin daren Talata.
Wata mazauniyar garin Rigasa mai suna Fatima ta bayyana cewa maharan sun far wa unguwan ne da misalin karfe 2 na dare dauke da manyan bindigogi.
” Sun fado gidanmu suka kwace wa ‘ya ta wayar ta sannan sai suka rika yi mana bincike kamar sun yi ajiya. Da na ci gaba da rokon su sai suka sharara mani mari suka nemi sai sun tafi da ni.
” Adaidai muna wannan jayayyane, ‘yan sanda suka iso suka fara artabu da maharan.
Shi ko mijin wanda aka yi garkuwa da matarsa mai suna Ibrahim ya ce tabbas maharan sun tafi masa da mata, amma basu tafi da jaririn su.
” Ni ma na arce ne da naji karan harbin bindiga, yadda Allah ya sa na tsira kenan.
Shi ko wani mazaunin garin cewa yayi sun shiga gidan sa sun tafi masa da kudi har Naira 450,000.
Rundunar ‘Yan sanda
kakakin rundunar ‘Yan sandan Kaduna Yakubu Sabo ya ce ‘yan sanda sun fatattaki wadannan mahara a daidai lokacin da suke aikata wannan ta’addanci.
” Ana yi mana waya muka far wa wannan gari inda muka yi artabu da wadannan mahara. Wasu da dama daga cikin su sun arce da rauni a jikin su. Sannan idan banda matan da suka yi garkuwa da babu wanda suka tafi da.
” Yanzu haka da nake muku magana jami’an mu suna cikin dazuka domin ceto wannan mata da suka tafi da ita.