Cikin talatainin daren yau Alhamis, mahara suka dira a garin Kanoma, suka kashe mutane 16. Haka jami’in gwamnati ya tabbatar.
Kanoma na cikin Karamar Hukumar Maru a jihar Zamfara. Maru ce aka bada sanarwar Gwamna ya dakatar da Sarki, a bisa zargin mu’amala da masu garkuwa da mutane.
Da ya ke magana a kan harin, Sakataren Yada Labarai na Gwamna Bello Matawalle, mai suna Yusuf Idris, ya ce mahara sun kai farmakin ne da karfe biyu na dare, ba da jijjifin safiya ba.
Ya ce ba su tsaya zaben wanda za su kashe ba, harbin kan-mai-tsautsayi suka rika yi, har sai da suka kashe mutane 16.
Karin bayanin da ya yi ya ce wasu da dama sun samu raunuka, kuma ana ci gaba da kulawa da su a Asibitin Gwamanatin Tarayya na Gusau.
Ya yi kira ga mazauna kauyuka da su rika bada rahotannin duk inda suka ji ko suka ga ciftawar mahara a cikin yankunan su.
Ya ce wannan sabuwar gwamnati ta maida himma wajen hawo kan kalubalen rashin tsaro a dukkan fadin jihar Zamfara.
Sa’o’i kadan bayan kai harin ne dai Idris ya bada sanarwar dakatar da Sarkin Maru, Abubakar Ibrahim mai mukamin Banaga na Maru, da kuma Dagacin Kanoma Ahmed Auwal, inda aka kai hare-haren.
Za su ci gaba da zama a matsayin dakatattu har sai bayan fitar da sakamakon kwamitin binciken da za a kafa.