MAHARA: Matawalle ya dakatar da sarkin Maru

0

A sanarwa da Darektan yada labaran gwamnatin jihar Zamfara Yusuf Idris ya fitar, gwamnan jihar Bello Matawalle ya dakatar da sarkin Maru Abubakar Ibrahim daga kujerar sarautar Maru.

Sanarwar ya ce gwamna yayi hakane bisa gano cewa sarkin na da hannu a ayyukan mahara da yayi wa jihar katutu.

Bayan haka kuma an dakatar da hakimin Kanoma, Ahmed Lawan shima bisa ga wannan zargi.

Bisa ga wannan sanarwa dukka wadannan sarakuna za su ci gaba da kaurace wa masarautar su har sai an kammala bincike game da wannan zargi.

A kwanakin baya ne gwamna matawalle yayi a rangama da mahara a hanyar sa ta zuwa garin Lilo yin ta’aziyya.

Masu tsaron gwamnan sun fatattaki wadannan mahara inda daga baya suka yi musu sabon shiri.

Share.

game da Author