MAHARA: An sako dan tsohon ministan kiwon lafiya

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta bayyana cewa an sako dan tsohon ministan kiwon lafiya Isaac Adewole.

Masu garkuwa da mutanen sun saki Dayo ne ranar Laraba. Sai dai babu tabbacin ko an biya kudin diyya kafin asako shi.

Idan ba a manta ba a ranar Talata da misalin karfe shida na yamma ne masu garkuwa da mutane suka sace Dayo a gonar sa dake kauyen Iroko a Ibadan.

Rundunar ta bayyana cewa an gano motar da wadannan masu garkuwa da mutane suka yi amfani da shi wajen sace Dayo daga baya.

A ranar Laraba kuma mataimakin sufeto janar dake kula da shiyyoyin Oyo, Osun da Ondo Leye Oyebade ya ce sun kama mutane uku da suke zargin suna da hannu wajen yin garkuwa da Dayo.

Wadannan mutane kuwa sun hada da Gbenga Ogunleye sabon direban Dayo, Sodiq Adebayo manajan gonar da wani ma’aikacin gonar.

Share.

game da Author