Ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Adamawa ta sanar cewa cutar amai da gudawa ko kuma cutar kwalara ya bullo a kananan hukumomi uku a jihar.
Wadannan kananan hukumomi kuwa sun hada da Yola ta arewa, Yola ta kudu da Girei.
Bisa ga sanarwan mutane 76 ne suka kamu da cutar inda a kananan hukumomin Yola ta arewa da Yola ta kudu mutane 44 sun kamu da cutar kuma mutum daya ya rasu sannan a karamar hukumar Girei mutane 31 sun kamu da cutar.
Ma’aikatar ta kuma kara da cewa ta hada hannu da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) da sauran kungiyoyin bada tallafi domin dakile yaduwar cutar a jihar.
Rigakafin Kwalara
Idan ba a manta ba kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa zuwa yanzu ta yi wa mutane akalla 377,000 allurar rigakafi cutar Kwalara a jihar Adamawa.
WHO ta gudanar da yi wa mutane allurar rigakafin ne ganin yadda cutar ta bullo a watan Mayu a kananan hukumomin Mubi ta Arewa, Mubi ta Kudu da Maiha a inda mutane da dama suka kamu da cutar.
WHO ta kuma gina asibitocin kula da mutanen da suka kamu da cutar na gaggawa a wannan lokacin kuma hakan ya san an samu ragowar wadanda suke fama da cutar da mace mace da aka yi ta fama dashi matuka.
” A wannan lokacin da cutar ta bullo a jihar WHO ta dauki ma’aikata 35 wanda ta biya daga aljuhunta domin inganta kula da mutanen da suka kamu da wannan cuta. Sannan ta samar da duk magungunan da aka yi amfani da su wajen kula da mutanen da suka kamu da cutar tare da wayar da kan mutane game da tsaftace muhallinsu da abincin su domin guje wa kamuwa da cutar kwalara’’.
A yanzu haka WHO na horas da zababun ‘Yan jarida da aka zabo daga jihohin Adamawa,Yobe da Barno domin a koya musu makaman aiki kan yadda za su rika dauko rahotanni yadda ya kamata musamman ya yankunan Gabashin Arewacin Najeriya.
ALAMUN KAMUWA DA CUTAR.
1. Zazzabi.
2. Amai da gudawa.
3. Rashin jin karfi a jiki.
4. Rashin iya cin abinci
5. Suma.
HANYOYIN GUJE WA KAMUWA DA CUTAR.
1. Tsaftace muhalli.
2. Wanke hannu da zaran an yi amfani da ban daki.
3. A guji yin bahaya a waje.
4. Amfani da tsaftattacen ruwa.
5. Wanke hannu kafin da bayan an ci abinci.
6. Cin abincin dake inganta garkuwan jiki.
7. Yin allurar rigakafi
8. Zuwa asibiti da zaran an kamu da cutar.