Kungiyar Masarautar Daura ya gudanar da Addu’o’i na musamman Allah ya ceto Magajin Garin Daura

0

Kungiyar Masarautar Daura ya gudanar da Addu’o’i na musamman domin Allah ya kawo karshen garkuwa da mutane da ake yi a kasar nan da kuma Allah ya dawo musu da magajin garin Daura, Alhaji Musa Umar.

Yau Lahadi yayi daidai da kwanaki 54 da da sace Magajin Garin Daura Alhaji Musa Umaru.

An gudanar da wannan Addu’o’i ne a makarantar firamare na Muhammadu Bashar dake garin Daura.

Shugaban wannan kungiya Abubakar Dantakai ya bayyanawa kamfanin dillacin labaran Najeriya cewa wannan addu’ a ya hada ne da wani dan garin Daura mai suna Abba Danbeza ma’aikacin Hukumar EFCC da aka dauke shima a hanyarsa ta zuwa garin Daura daga Legas,a Kano.

Ya ce ya zama dole a koma ga Allah domin yanzu fa abin ya ki gaba yaki baya.

” Kwanaki 24 kenan da dauke Danbeza amma ba a ji daga masu garkuwan ba.

Shima danuwan Magajin Gari, Musa Umar, Umar Umar ya bayyana cewa lallai akwai har yanzu basu ji daga Magajin Gari ba.

” Tunda aka zo har gida aka dauke Magajin Gari, kwanaki 54 kenan bamu ji komai ba daga bakin masu garkuwan. Bamu san ko wani hali yake ciki ba.

Yace ba kamar yadda ake ta yadawa ba cewa wai maharan sun kira ‘yan uwan Magajin Gari Umar da suka yi garkuwa da.

Bayan haka ya godewa mutanen garin Daura da sauran ‘yan Najeriya bisa ci gaba Addu’o’i da suke yi Allah ya sa a sako Magajin Garin.

An sauke Alkur’ani, anyi zikirori da huduba a wajen Addu’o’in.

Share.

game da Author