Kungiyar masanan magunguna na kasa (PCN) ya rufe manya da kananan shagunan siyar da magani 231 a jihar Nasarawa.
Shugaban kungiyar Stephen Esumobi ya sanar da haka a garin Lafia inda ya kara da cewa kungiyar ta yi haka ne bisa ga sakamakon binciken da ta gudanar a kan shagunan dake siyar da magunguna a jihar.
Matsalolin da ya sa PCN ta rufe wadannan shaguna sun hada da rashin tsaftace muhalli, rashin lasisi, rashin sabunta takardun da wa’adin su ya kare, siyar da jabun magunguna da rashin kwararren masanin magani a shagunan.
Esumobi ya ce shagunan da suka rufe sun hada da manyan shagunan siyar da magani 18 da kananan shaguna 213.
A kwanakin baya kungiyar masana magunguna ta Najeriya reshen jihar Adamawa (PCN) ta rufe manya da kananan shagunan siyar da magani 400 a jihar.
Jami’ar hukumar Anthonia Aruya wacce ta sanar da hakan wa manema labarai ta bayyana cewa sun yi haka ne domin bankado shagunan siyar da magungunan dake karya dokar kungiyar sannan da kawar da wasu ayyukan bata gari da suke yi ta hanyar siyar da jabun magunguna.
” Cikin laifukan da muka kama wadannan shagunan sun aikata sun hada da rashin tsaftace muhallin da shagunan suke, siyar da maganin da aka hana siyar wa a kasuwannin kasar nan, rashin lasisi da sauran su.
” A takaice dai mun rufe shagunan siyar da magunguna 400 sannan mun bar wasu 10 domin sun cika sharuddan kungiyar.”
A karshe Aruya ta bayyana cewa sun fara farautar irin wadannan shaguna ne domin kawar da masu gurbata na gari daga cikin su da kuma wadanda ke siyar da jabun magani a jihar.
Discussion about this post