KUDADEN KANANAN HUKUMOMI: Har yanzu akwai sauran rina a kaba tsakanin gwamnoni da kananan hukumomi, daga Kais Sallau

0

Babu shakka wannan tsarin da gwamnatin tarayya ta fito dashi na turawa kananan hukumomi kudinsu kai tsaye ba tare da yabi hanun gwamnoni ba abin a yaba ne, kuma zai ba shugabannin kananan hukumomin daman samun isassun kudade a hanunsu domin gudanar da aiki.

Ba shakka wannan tsarin ya samu karbuwa a gurin akasarin mutane kama daga ma’aikatan gwamnati musamman na kananan hukuma, harma wadanda ba ma’aikata ba. Kalilan mutane ne basu goyon bayan wannan tsarin saboda zaa rage musu hanyan satar kudin al’umma. Daman sun mayarda kananan hukumomin gurin tatsar nono saboda sunfi karfin wadanda aka basu gadin saniyar (shuwagabannin kananan hukuma). Amma yanzun sai da amincewar wanda aka basu gadin saniyar kafin zasu tatse nono. Amfa shi wanda aka basa gadin saniyar a ko da yaushe hukuma masu yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) zasu iya tuhumarsa yadda yayi dashi. Saboda haka shugabannin kananan hukumomi ayi hatara. Shugaban karamar hukuma zai iya cire kudin da gwamnatin tarayya ta turo masa ya kaiwa gwamna. amma yasan cewa zai iya zuwan kirikiri. Domin idan aka zo bincika babu ruwan gwamna.

Muhimman Abubuwa Kuda Ukun Da Gwamnatin Tarayya Zata Yi Kafin A Samu Cikakkan Nasara Kan Samun Yancin Kai Na Kananan Hukuma. Bayan Turawa Kananan Hukumomi Kudadensu Kai Tsaye Daga Gwamnatin Tarayya.

Akwai bukatar;

* Dole sai gwamnatin tarayya ta karbe zaben kananan hukuma daga hanun gwamnatin jihar.
* Haka kuma kotunan da zasu saurare korafin zaben kananan hukuma (Local Govt Election Tribunal) gwamnatin tarayya ce zasu kafa su kuma su turo alkalai.
* Sannan lokaci daya zaa dinga yin zaben kama daga shugaban kasa, gwamnoni, yan majalisun tarayya da na jihohi da kananan hukuma. Kuma su sauka tare. Ta yadda wakilai daga gundumomi (Councilors) ne kawai zasu iya tsige shugaban karamar hukuma.

Idan har aka samu aka aiwatar da wadanda abubuwa, to ba shakka kananan hukumomi sun samu cikeken yancin kai. Ta nanne shugaban karamar hukuma zaiyi mulki ba tare da tsaro ko barazana daga sama ba.

To, amma fa idan har zaa bar wadannan abubuwan karkashin gwamnoni, gwamna shi zai shirya zaben shuwagabannin kananan hukuma, shi zai gudanar da zaben a lokacin da yaga dama. Gwamna shi zai kawo wanda yaga dama, a lokacin da yaga dama, ya kuma ciresa a lokacin da yaga dama. To, mai kake tsammani? Gwamna yacewa shugaban karamar hukuma ya cire kudi ya kawo, shi kuma yace bazai kawo ba? Bayan gwamnan ya dasa shi. Dole zasu cire su kawowa gwamnan, kuma duk wanda yaki kawowa a tsige shi tunda ‘yan majalisun jihohi ‘yan anshin shatan gwamnoni ne.

Haka idan kana gadaran zabe akayi kaci, gwamna sai ya hada baki da alkalai kotu sauraran karan zaben su cire ka tunda suma shi ya nada su.

To, ya kamata gwamnatin tarayya tayi kokari da karbe wadannan abubuwan daga hanun gwamnatin jihar, ta nanne komai zai tafi daidai da ikon Allah. Domin debe kudaden kananan hukumomi da gwamnoni suke yi yana daya daga cikin abinda ya kara talauci a cikin al’umma. Idan har aka daidai kananan hukumomi, toh zaa samu sauki a sama.

Ina son gwamnoni su fahimci cewa fada da suke yi da wannan tsari na samun kudin kananan hukumomi kai tsaye daga gwamnatin tarayya, kaman suna fada da talakawa ne. Domin akasarin wadanda zasu amfana da wannan abin takawa ne. Domin shuwagabannin kananan hukumomi suke kusa da mafi yawan al’umma. Kuma su shuwagabannin kananan hukuma su suka fi sanin matsalolin al’umma tunda su suke tare dasu.
Allah ya tabbatar mana da mafi alkhairi.

Allah ya bamu zaman lafiya a kasarmu Najeriya. Ya bamu damina mai albarka.

Share.

game da Author