” Ku murkushe mana masu fitinar kasar nan mu huta” –Babban Hafsan Sojojin sama

0

Babban Hafsan Sojojin Sama, Sadiqque Abubakar, ya umarci Zaratan Musamman da aka kafa domin tunkarar kalubalen matsalar tsaro su fafata yakin a-yi-ta-ta-kare domin su murkushe duk wasu maso kawo wa kasar nan barazana.

Air Marshal Sadiqque ya ce su kau da kai daga farfagandar ’yan ta’adda da masu nuna musu tausayi, su murkushe su kawai.

Ya yi wannan kira ne a Abuja, cikin sakon sa na Barka da Sallah ga daukacin musulmi.

Bayan godiya ga Allah, Sadiqque ya kuma gode wa sojoji bisa irin juriya da kishi da kuma himmar su dangane da nasarorin da ake ci gaba da samu.

Ya yi bayanin cewa a yanzu akwai wadatar jiragen yaki da kayan aiki da kuma makamai. Sannan kuma akwai zaratan ko-ta-kwana wadanda a koda yaushe a shirye suke da su tunkari kowane irin kalubale.

Sannan kuma ya gode wa kwamandojin da ke bakin daga da jami’an da ke duba su.

Ya kuma gode wa iyalan sojojin da suka sadaukar da kan su a daidai wannan lokaci su na yaki domin samar da wanzuwar zaman lafiya a kasar nan.

A daidai wannan lokacin sallah, ya yi wa wadanda suka sadaukar da rayukan su addu’a da kuma fatan alhari ga iyalan su.

Ya ce Najeriya ba za ta taba mantawa da gagarimar gudummawar da suka bayar ba.

Share.

game da Author