Kotu a jihar Legas ta tsare wani Ustaz mai suna Abdulsalam Salaudeen, da akafi kira da Alfa a garin Legas bayan an zarge shi da yi wa wata yar shekara 5 fyade a masallaci.
Wanda ya shigar da karar Olanrewaju-Dawodu ya ce an kama wannan malami ne bayan wasu sun zargeshi da yi wa yara haka. Kuma wadanna yara ne da ke karkashin sa yana koyar da su.
A haka ne fa wasu suka saka kamara a harabar masallacin daga nan suka kamashi.
Sai dai duk da haka ya musanta wannan zargi, inda kotu ta ce a ci gaba da tsare shi sai an kammala bincike a kai.