Kutun da ke sauraren kararrakin zaben shugaban Kasa ta hana dan takarar shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da jam’iyyar damar bincikar rumbun tattara sakamakon zaben shugaban kasa na Hukumar zabe.
A hukuncin da kotun ta yanke ta ce babban dalilin da ya sa kotu ta hana kuwa shine ganin cece-kuce da ya tirnike tsakanin jam’iyyar PDP, Atiku da hukumar zabe inda INEC ke cewa basu da rumbun, su kuma suna cewa akwai rumbun.
Lauyan dake kare hukumar zabe INEC Usman Yunusa yace babu yadda za yi kotu ta amince da wannan kira na PDP da dan takaranta bayan kuma hukumar bata da irin wannan ‘Server’ da suke ikirarin za su duba.
Daga nan ne fa hukumar zabe ta yi watsi da wannan kira tace ba za a duba wani rumbu ba.
Karanta nan: Kila Aljanu ne suka loda wa Atiku kuri’u a ‘saban sa’ ba mutane ba
Atiku Abubakar ya yi ikirarin cewa ya fi Shugaba Muhammadu Buhari samun yawan kuri’u a zaben. Sannan kuma ya ce ya samu hujjar sa ne daga runbun na’urar da INEC ke killace alkalumman sakamakon zabe.
A lissafin da Atiku ya bayar a matsayin shaida a gaban Kotun Daukaka Karar Zabe, sun nuna kenan dukka gaba dayan kuri’un da aka tantance kakaf a jihohi 33, an jefa su ga Buhari da kuma Atiku kenan.
Tazgaro da rashin tabbas din ikirarin da Atiku ya yi, ya kara fitowa fili ne idan aka yi la’akari da cewa an samu kuri’un da aka soke sama da miliyan 1.2 a zaban na shugaban kasa.
Atiku dai yace ya bai wa Buhari tazarar kuri’u miliyan 1.6 a zaben shugaban kasa.
Karanta nan: BABBAR MAGANA: Jega ya yi magana a kan rudanin ‘server’
Discussion about this post