Babban kotu dake jihar Legas ta daure tsohon shugaban hukumar NIMASA bayan kama shi da akayi da laifi yin sama da fadi da naira Miliyan 139 a hukumar.
Hukumar EFCC ce ta maka Calistus Obi a kotu bisa zargin yin almundahana da kudaden hukumar har naira miliyan 139 watanni shida bayan nada shi.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya nada Obi watanni biyu bayan an rantsar dashi. A baya dama can shugaba Buhari ya nada sallami tsohon shugaban Patrick Akpobolokemi bisa rashin amincewa da aikin sa a hukumar.
Yanzu dai bisa ga hukuncin kotun, Obi zai yi zaman gidan yari har na tsawon shekaru bakwai.
Discussion about this post