” Ko APC ta saki Oshiomhole ya bi ruwa, ko kuma ruwa ya ci su tare – Minista Shittu

0

Ministan Sadarwa Adebayo Shittu, ya bi sahun jiga-jigan APC masu goyon bayan an cire Shugaban Jam’iyya Adams Oshiomhole.

Ya ce tantagaryar rashin adalcin da Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole ya shimfida a cikin jam’iyyar, shi ne ya janyo aka rasa jihar Oyo da ma sauran jihohin da APC ta sha kaye a zaben gwamnoni.

Da ya ke zantawa da PREMIUM TIMES a Abuja a ranar Litinin, Shittu ya ce idan jam’iyyar APC na so ta tsira da sauran guntun mutuncin da ya rage mata, to ta sauke Oshimhole daga shugabancin jam’iyyar kawai.

Shittu ya ce sauke Oshimhole ya zama wajibi idan har jam’iyyar APC na so ta sake cin zabe a 2023.

Da ya ke magana a kan hana shi takarar gwamna da aka yi a zaben fidda-gwanin APC, Shittu ya nuna cewa kamar alhalin sa ya sa APC din ta fadi zaben gwamna a Jihar Oyo.

ALLAH YA YI FUSHI DA OSHIOMHOLE

“Allah ne ya hukunta su, ya nuna musu su fa ba komai ba ne a Jihar Oyo. Ya kuma nuna wa shugaban APC cewa ba fa zai shuka rashin adalci kuma ya yi nasara ba.” Inji Shittu.

Shittu ya ce an yi masa rashin adalci da aka hana shi takara saboda dalilin bai je bautar kasa ba, wato NYSC, alhali shi ma tsohon gwamna Abiola Ajimobi bai yi NSYC din ba.

Daga nan ya ce ba wancan ne karo na farko da aka fara yi masa rashin adalci ba.

Ya ce ko a lokacin UPN an hana shi takarar majalisar jihar Oyo, saboda ya soki lamirin shugabannin jam’iyya na Oyo, haka kuma aka yin masa a cikin NPN duk a zamanin Jamhuriya ta Biyu.

“Haka yanzu aka yi min a zaben 2019. Na san na fi saura cancanta, saboda wasu dalilai da dama, amma aka yin min rashin adalci, aka hani takara.”

OSHIOMHOLE BA SHI DA AMFANI A APC

Da an tambaye shi dalilin da ya sa ya ke goyon bayan a kori Oshimhole daga shugabancin jam’iyya, sai ya ce, “Oshiomhole ne fa ya samu APC ta na rike da jihohi 26. Yayin da ya gama lalata jam’iyyar saboda ragabzar rashin adalci da gigiwar giyar mulki, da aka yi zaben 2019 sai APC ta tashi da jihohi 20. To tsoron da na ke ji shi ne kafin 2023, akwai alamon da ke nuna cewa APC za ta kara rasa jihohi idan ba a sallami Oshiomhole kafin 2023 ba.

“A yanzu haka Shugaba Muhammadu Buhari ne maganadisun da ke rike da jam’iyyar APC. Daga ranar da aka ce Buhari ya daina tsayawa takara, to Oshiomhole ba zai iya rike jam’iyyar ba. Ya zama dole ma mu sauke shi daga shugabanci, mu nada wanda ya san abin da ya ke yi, wanda zai yi mulki da kwakalwar sa, ba ratata sarkin surutai marasa kan-gado ba.”

Share.

game da Author