KIWON LAFIYA: Mazauna Abuja sun koma ga bokaye da gargajiya

0

Mazauna wasu garuruwan dake karkashen kulawar babban birnin tarayya, Abuja, sun ce sun gwammace su garzaya wurin Bokaye domin neman waraka ga cutukan dakan kama ‘ya’yansu maimakon zuwa asibiti.

Babban dalilin kuwa shine rashin asibiti kusa da su.

Wata likitar gargajiyya mai suna Fatima Yusuf ta ce ta dade tana duba yara sannan tana ba iyaye magani domin warkar da ‘ya’yan su iadn suka kamu da ciwo.

Fatima tace tana samo magungunanta ne a can cikin kungurmin daji. kuma a duk lokacin da ta ba yaro sai kaga ya samu sauki ya warke.

Haka shima wani dattijo mai suna Musa Sarki, ya bayyana cewa shine kusan babban likiti a wannan gari nasu.

” Na gaji wannan sana’a ne daga iyaye da kakanni. Hakan ya nine kawai zan iya hada surkullen da zai yi wa mara lafiya aiki. Mukan shiga can cikin kungurmin daji don nemo ganyayyakin da muke amfani da shi wajen hada magungunan.

Yara na warke wa sannan kuma iyaye na jin dadin maganin mu. Shi dai magungunan baya wuce idan mun hada sai aje gida a dafa a baiwa yaro.

Share.

game da Author