Idan dai ba a manta ba mun taba kawo muku wani rahoto na musamman game da yadda mata suka raja’a kacokan wajen amfani da kayan mata.
Shi dai kayan mata wani siddabaru ne da akan hada domin kara sha’awa ga mace da kuma musamman a wajen saduwa da mijinta ko wani makamancin haka.
Joshua Aribisala na Cocin Tabernacle of Glory Church ne yayi suka game da yadda mata suka koma kacokan wajen yin amfani ire-iren wadannan siddabaru.
” An rika tambaya na game da ingancin amfani da ire-iren wadannan siddabaru da ake kira wai kayan mata. Da tambayar ta yi yawa shine na yi bincike mai zurfi don sanin ko menene wannan abu da yadda ake hada shi.
” Abinda na gano ya bani mamaki domin kuwa ba abu ne da ya Cancanta maci mai bin addini Kiristanci ta rika amfani da shi ba.
” Akan ba mata wani irin siddabaru ne su rika ratayawa ko daurawa a kwankwason su ko kuma suna cusawa a gaban su cewa muddun aka sadu da su za a rika son adawo ko a maimaita.
Akwai wata da tace min wai kawarta ne ta bata wani jigida ta rika daura wa a kugunta cewa mujin ta zai rika kusantarta akai-akai saboda jin dadinta da zai rika yi.
” Tace bayan ta daina amfani da wannan jigida sai mijinta ya fara kaurace mata ya daina sha’awarta.
Bayan haka wani malamin gargajiya ya bayyana cewa lallai akwai surkullen da ake hadawa da irin wannan abubuwa da ake hada kayan mata da su da yake da hadarin gaske.
” Akan hada da asirce-asirce da saura su da daga baya sai kaga ana ta hulda da shaidanu da sunan wai ana so miji ya so ki ko kuma aji dadin saduwa.
Wani malamin addinin musulunci, Yakubu Umar, ya ce lallai akwai babban matsala game da amfani da ire-iren kayan da ake kira wai kayan mata.
Sai dai ya ce tabbas akwai kuma da matsalar wasu mazan domin wasu bibiyan mata da suke yi yayi musu yawa matuka sai kaga matan su na gida sunemi irin wannan siddabaru domin su karkato da hankulan mazajen su gare su.
Wata mata, Rakiya Adamu, mai shekaru 63 ta ce a zamannin da suke ‘yan mata akan basu irin wadannan hadi domin inganta zaman auren su da mazajen su. Amma yanzu fa an barnata abin matuka.
” Ana yi masa hadi da wasu abubuwa da ba haka ba, surkulle da hade-haden da ba haka ba. Amma ada gyada ne da Aya, da sauransu za a hada ana sha.
Discussion about this post