A dalilin harbo jirgin saman yakin Amurka da kasar Iran ta yi shugaban kasar Amurka Donald Trump ya aika wa kasar da wasikar ta kwana fa fa shirin yaki.
Wasikar wadda Amurka ta aika da ita ta kasar Oman tana neman kasar Iran ta gaya mata dalilin da ya sa haka kawai zata harbo mata jirgi.
Kasar Iran ta musanta cewa da gangar ta harbo wannan jirgi cewa jirgin ya biyo ta sararin samaniyyanta ne.
Amurka ta ce wannan jirgi bai isa sararin samaniyyar kasar Iran din ba ta bugo shi kasa.
Tuni dai Iran ta aika wa majalisar dinkin duniya bayanan yadda abin ya faru da kuma daidai inda jirgin ya bi kafin suka bugo shi kasa.
Yanzu dai kasar Iran ta ce ba za ta maida wa kasar Amurka amsar sakon ta ba sai abin da shugaban addini na kasar Ayatullah Khomeini ya ce.
Shi dai Trump ya ce lallai fa Kasar Iran tw tafka kuskure.