KARRAMA ABIOLA: Buhari ya kunyata Obasanjo -Fayose

0

Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose ya soki tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo saboda kin karrama Mashood Abiola da ya yi.

Fayose ya ce Obasanjo bai kyauta ba da ya shafe shekaru takwas ya na shugabancin kasar nan, ba tare da ya karrama Abiola ba.

Daga nan sai ya ce karramawar da Shugaba Muhammadu ya yi wa Abiola ta kunyata Obasanjo.

Fayose ya bayyana haka jiya a shafin sa na twitter ce kamata ya yi Obasanjo ya karrama Abiola a matsayin sa na Bayarabe dan uwan sa a lokacin da ya shafe shekaru takwas ya na mulkin Najeriya.

Obasanjo ya yi mulki daga 1999 zuwa 2007. Shi ne shugaba na farko na farar hula tun bayan da soja suka maida wa farar hula mulki a cikin 1999.

Abiola ya fito takarar shugaban kasa karkashin SDP a zaben 1993. Ya yi takara tare da Bashir Tofa na NRC.

Ya ci zabe sai dai kuma gwamnatin soja ta Janar Ibrahim Babangida ta soke zaben tare da kin bayyana sakamakon.

A karshe an kulle Abiola a lokacin mulkin Sani Abacha, inda daga bisani ya mutu a kurkuku.

Gwamnatin Buhari a cikin 2018 ta yanke shawarar karrama shi, tare da maida ranar zaben 12 Ga Yuni ta zama Ranar Dimkoradiyya ta Kasa.

“Ina jinjina wa Buhari saboda karrama Abiola da ya yi. Amma abin kunya ne ga Obasanjo, wanda shi ne ya fi kowa cin moriyar rikicin 12 Ga Yuni, 1993, a ce ya shafe shekaru takwas ya na mulki ba tare da karrama Abiola ba.” Cewar Fayose.

Share.

game da Author