Wani abin alfahari da murna ga mutanen jihar AkwaIbom a auku a yau shine jirgin saman fasinjoji na farko ya tashi daga jihar zuwa Legas da Abuja.
Wannan shine karo na farko da wata jiha a kasar nan za ta fara yin sana’ar jigilar fasinjoji na jirgin sama mallakin jihar.
A yar gajeruwar buki da aka yi a filin jirgin saman jihar, Mataimakin gwamnan jihar Moses Ekpo ya bayyana wa mutane cewa wannan shine karon farko da za a samu haka a wani jiha a kasar nan.
” Zamu rika jigilar fasinjoji daga jihar mu AkwaIbom zuwa Legas da Abuja. Daga nan kuma zamu ci gaba da karo jirage. Idan har Kasar Ethiopia zata iya harka hada-hadar fasinjoji na jiragen sama, babu abin da zai hana mu iya yin nasara akai.
Wani fasinja, kuma tsohon kwamishinan jihar Charles Udoh ya ce ya dauke su tsawon mintuna 45 daga Uyo zuwa Legas.