Burin jam’iyar APC ya cika, bayan da ta kafa shugabanci a majalisar dattijai da wakilai.
Wannan babbar nasara ce ga gwamnati mai ci, kuma babban kalubale ne a wajenta tunda talakawa zasu zira mata ido don ganin mai zata iya yi na cigaban kasa.
Kasancewar shugabannin majalisa a cikin jam’iyar APC zai ba wa gwamnatin Buhari damar yin abun da yake so saboda tuwona maina za ayi.
A wance zangon (tenure) na mulki an samu rashin daidaito tsakanin bangaren da yake yin doka (National Assembly) da bangaren zantarwa (Executive).
Tasowar rikicin cikin jam’iya ne yayi sillar ficewar shugabannin majalisar guda biyu (Sen Abubakar Bukola Saraki da Hon Yakubu Dogara) daga jam’iyar APC zuwa PDP.
Tabbas, fitarsu daga jam’iyar APC ya bawa Buhari tasgaro wajen samun sahalewarsu don gudanar da wasu ayyuka na cigaban kasa kamar yadda shi Shugaba Buharin yace. A karshe ma har yake kiransu ba ‘yan kishin kasa ba.
A kwana a tashi, wannan maganar tazo karshe, babu maganarsu akan kujerar shugabancin majalisa. Daya daga cikinsu ma bai ci zabe ba don haka babu shi a majalisar tarayya yanzu.
Labudda, babu wata matsala da gwamnati zata fake da ita daga majalisar tarayya duba da yadda Buhari ya goyi bayan samun nasarar wadanda ya yadda dasu saboda su taimaka masa ya gina sabuwar Najeriya.
Mu dai ido ne namu, talaka ya gama nasa tunda ya zabi Buhari sau biyu, saura jiran gwamnatin Buhari ta saka masa da alheri, don kowa yaci ladan kuturu dole yayi masa aski.
A kasar Najeriya babu irin gudunmuwar da talaka bai bayar ba wajen tabbatar da Buhari a kujerar mulki. Cikin ikon Allah, talakawan suna shan wahala amma suna ihun ‘Sai Buhari’.
Yakamata Shugaba Buhari ya biya soyayyar da talakawa suke masa ta hanyar canza musu rayuwa da ikon Allah.
Duk da cewa kamar yadda na ta6a fada a wata jarida a baya, soyayyar yanzu ta ragu saboda jinkiri da aka samu wajen cika alkawarukan zabe a shekara ta 2015.
Wasu daga cikin talakawan sun samu ‘Crises and frustration of expectations’. Akwai wadanda suka cire rai da samun abin da suke zato daga Buhari amma duk da haka akwai da yawa da suke tare da soyayyarsa a zuci.
Fatan da nake yi, Allah yasa gwamnati kada ta kunyata wadannan masoyan gasken. Don da yawa daga cikin ‘yan Najeriya sun wanke kwano da cokula suna jiran shan romon dimokaradiyya.
Qalubale ga Shugaba Buhari, saboda mutane da yawa sun zira masa ido a wannan zangon mulkin na biyu fiye da na farko. Zango na farko ya qare cikin kar6ar uzurin gwamnati amma yanzu babu wannan maganar a wajen talaka.
Musamman ‘yan Arewa da suke ganin kamar duk ayyukan cigaba kudancin Najeriya aka yiwa a zangon farko. Gaskiyar lamari za a zira ido wajen ganin abin da Arewa zata samu daga 2019 zuwa sama.
Saidai abin mamaki naji shugaba Buharin cikin karsashi yana bayar da tabbacin za a sha romon dimokaradiyya a wannan lokacin. Lallai kam talaka yana jiran wannan romo da cokalinsa a hannu.
Allah yasa mu ga alheri.