JA DA BAYA-BAYA BA TSORO BANE: Maikon harin zamu kakaba wa Iran takunkumi mai tsanani – Inji Trump

0

Shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya bada sanarwar janye umurnin kai wa kasar Iran hari da ya bada tun a safiyar Alhamis a saboda wasu dalilai da ya ambato.

Shi dai Shugaba Trump ya bada umurnin a kai harin jiragen sama akan wasu sansanonin da suka hada da wuraren da kasar Iran ke girke makamanta masu linzamai, kayan yaki da sauransu kafin ya canja shawara cewa a dakatar da hakan.

Babban dalilin da Trump ya bada kuwa shine wai harin zai iya yin sanadiyyar rayukan mutanen da basu ji ba basu gani ba akalla 150 ko ma fiye.

A cewar Trump wannan shine babban dalilin da ya sa ya janye wannan hari.

Sai dai kuma Trump ya ce Amurka ba za ta zuba wa Iran ido ba wai shikenan. Ya ce za ta tsawwala matakan takunkumin da ta kakaba wa kasar ta inda kasar za ta shiga kangi mai tsanani.

Sannan kuma zai yi zama na musamman da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya domin tattauna batun.

Ita dai Iran ta ce ba ta da wani bayani da zata yi wa kasar Amurka domin ita ce ta fado mata sararin samaniyyarta batare da sallama ba cewa hakan ya sabawa dokar tsaro na kasa da kasa da ke rubuce a kundin majalisar dinkin duniya.

Sannan kuma ko da Trump yayi barazanar kai mata hari tace bata da na cewa sai abin da shugaban ta Ayatullah Khomeini ya ce.

Iran bata maida masa da amsa ba.

Share.

game da Author