Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta karbi naira bilyan 1.47 domin gyaran kwamfutoci da gina rumbun ajiyar bayanai kafin zaben 2019.
Binciken da jaridar PREMIUM ya gudanar ne ya tabbatar da cewa INEC ta karbi kudaden.
Sai dai kuma Premium Times ba ta tabbatar da shin an gina rumbun ajiyar alkaluman zabe da kudin ba ko kuma ba a gina ba?
Wannan tabbataccen bincike ya zo ne a daidai lokacin da ake ja-in-ja da INEC cewa ta na da ‘server’, wato rumbun da ta tattara sakamakon zaben Shugaban Kasa na 2019.
Dan takararar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kai karar rashin amimcewa da sakamakon zaben 2019. Sannan ya yi ikirararin cewa sun yi leken asiri a cikin rumbun ajiyar sakamakon zabe na INEC, wato ‘server’, kuma suka ga alkaluman zabe sun nuna Atikun ne ya yi nssara, ba Buhari ba.
Yayin ita kuma INEC ta karyata Atiku da PDP cewa ba ta mallaki ‘server’ ba. Kuma ta nemi Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa cewa ta kori karar da Atiku da PDP suka kai.
Premium Times ta tabbatar cewa INEC ta karbi kudin aikin ‘server’, wanda da farko naira bilyan 2.27 ta nema, amma aka ba ta naira bilyan 1.47.
Kakakin Yada Labarai na INEC, Festus Okoye, ya yi wa PREMIUM TIMES karin bayanin karbar kudin. Ya ce INEC ta nemi kudin ne a bisa tunanin ko da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai sa hannu a kudirin yin gyaran dokar zabe, wadda za a tattara komai ta tsari na zamani.
KIRI DA MUZU
Kungiyar Sa-ido kan Zabe, wato YIAGA, ta tabbatar wa PREMIUM TIMES jami’an ta sun ga jami’an INEC sun tattara kashi 65 bisa 100 na sakamakon zaben da suka tattara, a mazabun da YIAGA ta yi aikin sa-ido. Wato sakamako sama da 900 daga sama da 1400.
Kolacin da aka daga zabe da sati daya, Kwamishinan Zabe na Jihar Akwa Ibom, Mike Igini, ya shaida cewa za a tattara sakamakon zabe a ‘server’, wato rumbun ajiyar sakamakon zabe.
Akwai wata naira milyan 157 da INEC ta karba domin aikin kun-ji-kun-ji da lodin tarkacen ayyuka a intanet.
Amma INEC ta tsaya kai-da-fata cewa ba ya tattata sakamakon zabe kamar yadda Atiku ya yi ikirari a ‘server’ ba.
Jama’a na ta tofa albarkacin bakin su dangane da wannan sa-kota-sa-katsi. Sanata Shehu Sani ya ce abin kamar akwai borin-kunya ko kuma nannade tabarmar kunya.
Sannan ya ce shin Majalisar Dattawa ai ta san idan INEC ta karba ko ba ta karba ba.
Da dama na mamakin yadda INEC ta karbi kudin aikin ‘server’, amma kuma a yanzu za ta ce ba ta gina ‘server’.