Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga gwamnonin kasar nan da su tilasta wa yara da iyayen su tsarin saka yara makaranta na dole.
Hakan inji Buhari, ya zama wajibi kan kowane yaro ya samu ilmin firamare da na sakandare.
Wannan tsari ya na nuni da cewa za a iya kama iyayen da suka ki tura ‘ya’yan su makaranta tare da gurfanar da su a gaba shari’a domin a hukunta su.
A karkashin Shirin Koyar da Yara Ilmi a Matakin Farko, dokar 2004 ta tilasta cewa laifi ne ga iyaye su ki tura yaran su makaranta har zuwa aji uk (JSS3) na sakandare.
Haka wannan doka ta Shashe na 2(2) ta jaddada cewa “kowane iyaye su tabbata dan su ko ‘yan su ta yi (a) Karatun firamare har ta kammala (b) Akalla aji uku na karamar sakandare.”
Sannan kuma a Sashe na biyu na wannan doka ta ce za a iya kama uban da ya ki saka ‘yar sa makarantar firamare ko sakadare, tare da tarar naira dubu biyu ko dubu biyar idan wata daya ne ko wata biyu yaron ya yi fashin zuwa makaranta, ko kuma daurin wata daya ko wata biyu.”
Wannan jawabi na Buhari ya zo ne watanni kadan bayan Ministan Ilmi Adamu Adamu ya sha gargadin iyaye cewa gwamnati za ta fara daure wadanda ba su kai yaran su makaranta.
Adamu ya ce akwai abin takaici ganin dimbin yaran da ke gararamba a kan titinan Najeriya.
Najeriya ce ta fi sauran kasashen duniya yawan dandazon yaran da ba su zuwa makaranta.
Akwai yara milyan 13.2 da ke gararamba a kan titinan kasar nan.
Kididdigar Hukumar UBEC ta Kasa ce ta tabbatar da haka cikin Oktoba, 2018.
Discussion about this post