Hukumar USAID zata tallafa wa Najeriya da dala miliyan 243

0

Ofishin jakadancin kasar Amurka ta ce Hukumar USAID zata tallafa wa Najeriya da dala miliyan 243

Za yi amfani da wannan kudade ne a fannonin ayyukkan noma, ilimi, da kiwon lafiya a Najeriya.

Daga cikin wannan kudi dala 165 zai shiga aljuhan ma’aikatan kiwon lafiya domin inganta kiwon lafiyar mata da yara kanana, kawar da zazzabin cizon sauro,tarin fuka da yunwa a jikin yara kanana.

Dala miliyan 25 zuwa ma’aikatan Ilimi domin inganta ilimin bokon a makarantun yankin arewa sannan dala miliyan 22 a ayyukan noma.

Za a yi amfani da dala miliyan 21 wajen inganta aiyukkan siyasa, ayyukan gwamnati, kungiyoyin kare hakin dan adam da sauran su.

Jami’in USAID, Stephen Haykin ya bayyana cewa Najeriya ta sami wannan tallafi ne a dalilin yarjejeniyyar da gwamnatin Amurka ta yi da kasan.

Haykin yace tallafin zai ci gaba daga nan har zuwa 2020.

A kwanakin baya ne USAID ta ware dala miliyan 225 domin tallafa wa fannin kiwon lafiyar jihohi biyar a kasar nan.

Jami’in USAID Stephen Haykin ya sanar da haka a wani taro da suka yi a Abuja.

Haykin ya ce USAID za ta fara inganta fannin kiwon lafiyar jihohi uku daga cikin biyar a kasar nan.

Wadannan jihohi kuwa sun hada da Bauchi,Kebbi da Sokoto.

“USAID za ta tallafa wa wadannan jihohin ne ganin yadda sakamakon bincike ya nuna cewa mutanen wadannan jihohin na fama da matsalolin rashin kiwon lafiya na gari.

“Za mu fi bada karfi wajen inganta kiwon lafiyar mata da yara kanana a wadannan jihohi domin rage yawan mace macen mata da yara kanana.

Share.

game da Author